Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-01 20:35:44    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Asalam alaikum jama'a masu sauraro, barkanmu da wr haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan sabon shiri na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin wanda mu kan gabatar da shi a ko wane lahadi domin shere ku.Muna fatan za ku ji dadin shirin. Sai ku kutso akwatin rediyonku ku saurara.

Barayi sun yi wa mai gadi sata. Mr Jing Buchun yana da shekaru sittin da haihuwa,yana aiki a matsayin dan gadi mai sa kai ga kauyen da yake zama a ciki cikin shekaru sama da ashirin da suka gabata domin kare kauye daga barayi. Tun daga shekara ta 1987 ne ya fara yawon sintiri a kauyen da dare tare da wata fitila ya kuma yi kuwwa ga kauyawa da su sa hankali kan barayi. Cikin shekaru sama da ashirin da suka shige,dukkan gidajen kauyen sun sami tsaro mai kyau ban da na mai gadi Jing. A wata rana da dare a watan jiya wasu barayi sun shiga gida mai gadi sun yi masa sata yayin da yake yin sintiri a waje.

Ashe bom ne na iya tashi. An sami wani mutum a birnin Shijiazhuang,babban birnin lardin Hebei dake arewancin kasar Sin da ya gano wani abin cylinder yana tsammanin abin cylinder na daukar iskar Oxygen sai ya tafi da shi gida. Ya ajiye shi a gida yana neman sayar da shi. A ranar lahadin da ta shige,wani abokinsa mai arziki ya zo gidansa ya gano wani abin cylinder a kwance a dakin barci.nan take ya sanar da 'yan sanda. Da 'yan sanda sun isa wurin,sun yi bincike cikin nituswa. Daga baya sun gane cewa ashe wani bom ne da ke iya tashi ko wane lokaci. 'Yan sanda sun sanar da jama'a idan sun sami wani abun da ba su iya gane shi mene ne ba sai su kira 'yan sanda.

Wani uba ya mika kansa ga 'yan sanda. An sami wani mutum da ake kiransa Li Fan da matarsa a birnin Tumen na lardin Jilin dake arewa maso gabacin kasar Sin da suke daukar dansu yayin da ya ke jariri.suna kaunar dansu kwarai da gaske har fiye da kima,sun shagwaba shi yayin da yake girma. Bayan wasu shekaru,dansu ya fara shan giya bayan da ya koma gida da duka ubansa har ma ya lalata kayayyakin gida. A ranar laraba da ta shige,ubansa ya kashe dansa sannan ya tafi ofishin 'yan sanda ya mika kai.yanzu ofishin 'yan sanda na fara binciken batun.

'Yan sanda sun tsare wani fasinja. A ranar lahadi da ta shige a filin jiragen sama na birnin Shenyang dake lardin Liaoning dake arewa maso gabacin kasar Sin,'yan sanda sun kama wani fasinja namiji mai suna Wang saboda ya yi yunkurin shiga jirgin saman dake wurin. Wannan dan fasinja da wasu sun yi fushi da suka ji an sha dakatar da tashin jirgin saman fasinja sau da dama,har sun yi cacar baki da mahukunta da yin fada da su. Da ganin haka 'yan sanda a filin sun zo sun kama wadannan fasinjojin.

Wani mutum ya fadi daga taga saboda sumba. An sami wani mutum da ya ji rauni bayan da ya fadi daga wata taga a bene na biyu na wani gini a birnin Zhengzhou na lardin Henan na kasar Sin. Ginin nan yana gefen hanyar Hongzhuan.Wata tsohuwa mai suna Kou ta ji wata kara,sai ta leka ta taga, sai ga ta ga wani mutum a kwance a kasa. ba tare da bata lokaci ba wata ya mata ta zo wurin ta ba da taimako ga mutumin nan a kwance. Daga baya tsohuwa Kou ta gane cewa,matarsa ne,su biyu suna zama a saman gidanta. Wannan mutum ya fadi ne yayin da ya sumbaci matarsa a taga.

Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin.Mun gode muku saboda kun saurarenmu.(Ali)