Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-01 20:35:16    
Bunklasuwar jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui

cri

Jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin da kanta ta kabilar Hui tana arewa maso yammacin kasar Sin, tana daya daga cikin jihohin cikin gida da muraba'insu sun fi rashin fadi na kasar Sin, ita ce kuma shiyyar kabilar Hui mai ikon aiwatar da harkokin kanta daya kawai ta kasar. Mutane fiye da miliyan 6 suna zama a wannan shiyyar da ke da fadin muraba'in kilomita dubu 60, cikin kashi 1 cikin uku su ne musulmi kabilar Hui. A cikin shirinmu na yau, mun gayyaci Mr. Wang Zhengwei, mukaddashin shugaban jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui don ya gabatar muku da hanyar bunkasuwar jihar Ningxia, inda za ku ji labari game da jama'ar kabilu daban daban na jihar da suka hada gwiwarsu don kafa "Jihar Ningxia mai kere-kere".

Tun da da da can, jihar Ningxia wata jiha ce mai kabilu da yawa, da hadin kan al'adu, da kuma wadatuwar kasa. Mr. Wang Zhengwei, mukaddashin shugaban jihar Ningxia ya ce, "Ko da ya ke jihar Ningxia wata karamar jiha ce, amma a waje daya kuma ita ce wata babbar jiha wajen albarkatu. Tana nuna fifiko wajen albarkatun sha'anin noma, da kwal."

Amma, sabo da jihar Ningxia tana yammacin kasar Sin, kuma tana rashin fadi, don haka, ana kasance da babban gibi a tsakaninta da yankin da ke gabashin kasar a fannin saurin bunkasuwa da skelin tattalin arziki. Sabo da haka, a lokacin da kasar Sin ke soma aiwatar da dabarar bunkasuwar yankin da ke yammacin kasar a 'yan shekarun da suka wuce, bisa abin musamman nata, jihar Ningxia ta gabatar da makasudin bunkasuwarta, wato "Karama kuma mai wadata, karama kuma mai karfi, karama kuma da kyau". Jihar Ningxia ta kyautata aikin masana'antu, har ma ta zama muhimmin yankin da aka haka kwal na kasar Sin, a sakamakon gine-ginen sansanin masana'antun makamashi na Ningdong da ake yi a jihar, wato sansanin masana'antu na kwal da ya yi girma a Asiya. An kira wannan aiki ne na "Aiki mai lambar daya", jimlar kudin da za a bayar a kai za ta wuce RMB biliyan 300.

Mr. Wang Zhengwei ya bayyana cewa, neman fifiko da kyautata aikin masana'antu shi ne dalili na farko na gina wannan sansanin masana'antu.

"Bayan da gwamnatin tsakiyarmu ta bayar da ra'ayin neman bunkasuwa ta hanyar kimiyya, yaya za a juya hanyar bunkasuwar tattalin arziki ta jihar Ningxia, wannan dai ya zama muhimmin batun da muke tunani. Mun yi ta yin nazari har 'yan shekarun da suka wuce, a karshe dai mun tsaida kudurin mayar da aikin raya sansanin masana'antu na Ningdong zama aiki mai lambar daya na jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur."

Sansanin masana'antun makamashi na Ningdong ya riga ya jawo jari daga manyan masana'antu na gida da na ketare, tun bayan da aka soma gine-ginensa a shekarar 2003, hakan kuma sana'o'in samar da lantarki, da kwal, da dai sauransu suna samun bunkasuwa a hankali a hankali a Ningxia. A waje daya kuma, jihar Ningxia tana mayar da kiyaye muhalli a matsayin farko.

Bugu da kari kuma, manyan ayyuka na kauyuka a jihar sun samu kyautattuwa sosai, yawan kudin da manoma suka samu yana ta karuwa.

Mr. Wang Zhengwei ya gayawa wakilinmu cewa, yanzu yana tunanin batun zaman rayuwar jama'a, yana fatan jama'ar jihar Ningxia za su iya kece raini daga wajen sakamakon da gyare-gyare da bunkasuwa ke kawowa.

A 'yan shekarun da suka wuce, yawan mutanen da suka yi yawon shakatawa a jihar Ningxia ya yi ta karuwa, hakan ya kawo bunkasuwar tattalin arziki ta jihar. Bayan haka kuma, jihar Ningxia ta shirya bikin abinci da kayayyaki na musulmi har sau biyu, ta jawo kasashe fiye da goma daga Asiya, da Afrika, da kuma Amurka ta kudu. Ya zuwa shekarar 2010, yawan tsawon manyan hanyoyi na jihar Ningxia zai kai kilomita 1100, Ningxia za ta zama muhimmiyar shiyyar da ke hade da yankunan arewa maso yammacin kasar Sin da na gabashi maso tsakiyar kasar, ko shakka babu za ta kara samun bunkasuwa.