Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-01 19:54:15    
Abokanmu na Nigeria sun taya murnar ranar sauran kwanaki 100 shirya gasar wasannin Olympic na Beijing

cri
A ran 30 ga watan Afrilu, yayin da Sinawa suke kidaya kwanaki 100 da suka rage da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing, abokanmu na kasar Najeriya sun kuma shirya bikin murnar ranar sauran kwanaki 100 da suka rage da gasar a birnin Ikko.

A lokacin da suke murnar kasaitattun bukukuwa, 'yan Nijeriya su kan rera wakoki da taka raye-raye domin taya murna. Ran 30 ga watan Afrilu, rana ce ta yau da kullm kawai a kan kalandar Nijeriya, amma wannan ranar 30 ga watan Afrilu ya zama wata ranar da 'yan Nijeriya suka taya murma domin gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Mr. Otunba Sowale, wanda ya shirya wannan bikin taya murnar ranar sauran kwanaki 100 da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing wani Oba ne na jihar Ogun ta Nijeriya. Ya ce, yana son nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing a wannan rana ta musamman. "Ina tsammani, taya murnar irin wannan bikin da ke da nasaba da dukkan kasashen duniya abu ne mai ban sha'awa. Abin musamman da ya kamata a ambata shi ne, mu 'yan Nijeriya muna goyon bayan gasar wasannin Olympics ta Beijing. Taya murnar ranar sauran kwanaki 100 da suka rege da gasar wasannin Olympics ta Beijing nauyi ne da ke bisa wuyanmu. Ba ma kawai muka kishin gasar wasannin Olympics ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne, mu abokai ne na Sinawa. Makomarmu tana da hulda sosai da Sinawa."

A hakika dai, yau da makonni 3 da suka gabata, Mr. Otunba Sowale ya taba kawo wa kasar Sin ziyara. "A kwanan baya, na kai wa Beijing ziyara. Yanzu tituna manya ko kanana na birnin Beijing sun kara samun kawatarwa. A dukkan wuraren da ka isa, za ka ga alamar gasar wasannin Olympics ta Beijing. An kuma kawata duk birnin. Tabbas ne kasar Sin tana da karfinta wajen cin nasarar shirya wannan kasaitacciyar gasar da za ta jawo hankulan duk duniya."

Yanzu, birnin Beijing yana share fagen maraba da zuwan baki, wato 'yan wasannin motsa jiki da jami'ai da masu yawon shakatawa da 'yan jaridu da suka zo daga sauran kasashen duniya. Mr. Edwin Akalonu, wani dan jaridar "Vanguard" ta kasar Nijeriya na daya daga cikinsu. A watan Satumba na shekarar bara, ya taba yada labaru game da gasar kwallon kafa ta mata da duniya da aka shirya a nan kasar Sin. A gun gasar wasannin Olympics ta Beijing, zai yada labaru game da gasannin dambe da daga nauyi da kokuwa. Ya ce, bayan ya gama aikin yada labaru, yana fatan zai iya samun damar kai ziyara a yankuna dadan daban na kasar Sin. "A wannan ziyarata a kasar Sin, ina fatan zan iya samun damar kai ziyara a wasu kananan garuruwa ko wasu kauyuka. Ina son kara sanin al'adun kasar Sin ko da yake na riga na san wasu a lokacin da nake yada labarun gasar kwallon kafa ta duniya da aka shirya a kasar Sin a watan Satumba na shekarar bara."

Ko da yake galibin 'yan Nijeriya ba su da damar kallon gasar wasannin Olympics ta Beijing, amma suna kishin gasar wasannin Olympics. Samson Oluwole, wani dalibin jami'a ne, ya ce, ko da yake ba shi da damar zuwa Beijing, amma yana da imanin cewa, Beijing zai kawo wa sauran kasashen duniya abubuwa masu farin ciki. "Ina fatan za a iya ganin wata gasar wasannin Olympic ta Beijing mai ban sha'awa da za ta sha bamban sosai da sauran gasannin wasannin Olympics da aka shirya a da. Ina fatan za a ga murmushi a kan fuskokin jama'a. Sada zumunci abu ne mafi muhimmanci ga gasar wasannin Olympics. Ina fatan za a iya yada ruhun Olympics kamar yadda ya kamata. Ina cike da imanin cewa, duniyarmu za ta kara samun kyautatuwa a nan gaba."