Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 21:42:48    
Fararen hula na wurare daban daban na kasar Sin sun maraba da ranar da aka rage sauran kwanaki 100 da yin gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Ran 30 ga wata, rana ce da aka rage sauran kwanaki 100 da yin gasar wasannin Olympics ta Beijing. A birnin Beijing da kuma sauran birane na kasar Sin, an shirya bukukuwa iri daban daban domin maraba da zuwan gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A ran nan da safe, an kira babban taro na kara kwarin gwiwa kan sauran kwanaki 100 da yin gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008, kuma Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya halarci taron. Wakilai fiye da 6000 na sassan kiwon lafiya da ba da ilmi da motsa jiki da dai sauransu na birni Beijing su ma sun halarci taron. A gun taron, Liu Qi, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya rarraba ayyuka na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing da kuma hukumomi daban daban na Beijing a cikin kwanaki 100 masu zuwa.

A ran nan da safe, an shirya harkar gudun Marathon a cibiyar Olympics ta Beijing. Fararen hula kusan dubu 10 da kuma wasu baki masu sha'awar guje-guje na dogon zango sun shiga harkar.

Tare da zuwan gasar wasannin Olympics ta Beijing, fararen hula na kabilu daban daban na jihar Tibet ta kasar Sin suna ta kara mai da hankali a kan gasar. A ran 30 ga wata, fararen hula na jihar Tibet fiye da 3000 sun taru a filin wasannin motsa jiki na jami'ar Tibet don yin bikin murnar zuwan sauran kwanakin 100 da yin gasar wasannin Olympics. (Kande Gao)