Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 21:15:41    
Hong Kong ta yi gaggarumin biki domin maraba da wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Ran 30 ga wata misalin da karfe 4 da yamma, hukumar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ta yi gaggarumin biki a fili da ke gaban cibiyar al'adu ta Tsim Sha Tsui ta Hong Kong domin maraba da wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing, wadda ta yi kwanaki 37 tana zagaya dukkan nahiyoyi 5 na duniya, ta dawo kasar Sin.

A gun bikin, shugaban sashen ayyukan hukumar Hong Kong Mr. Henry Tang Ying-yen ya yi jawabi cewa, wutar wasannin Olympic ita ce alamar koli ta wasannin Olympic, kuma ta alamantar da fata da buri, da kuma haske da zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa, Hong Kong za ta tabbatar da ganin za a mika wa juna wutar yadda ya kamata. A matsayinta na zango na farko a kan hanyar mika wa juna wutar a kasar Sin, yanzu Hong Kong a shirye take. A ran 2 ga watan Mayu, Hong Kong za ta nuna wa dukkan kasashen duniya kyan ganinta da ruhunta bisa sigogin musamman nata.(Tasallah)