Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 19:50:14    
An kira babban taro na kara kwarin gwiwa kan sauran kwanaki 100 da yin gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri

Yau wato ran 30 ga wata, rana ce da aka rage sauran kwanaki 100 da yin gasar wasannin Olympics ta Beijing, a ran nan da safe, a babban dakin taruwar jama'a na Beijing. An kira babban taron kara kwarin gwiwa kan sauran kwanaki 100 da yin gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008. Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya halarci taron.

A gun taron, Liu Qi, shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing ya rarraba ayyuka na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing da kuma hukumomi daban daban na Beijing a cikin kwanaki 100 masu zuwa. Kuma ya nuna cewa, ya kamata a kara sa kaimi ga ayyukan ba da hidima na gasar wasannin Olympics ta Beijing da kuma gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing, da kara koyar da mazaunan Beijing a fannin ladabi, da kuma inganta hadin gwiwa tare da kwamitocin kula da wasannin Olympics da kuma wasannin Olympics na nakasassu na duniya domin kara yin kokari wajen shirya wata gasar wasannin Olympics da ke da halin musamman da kuma matakin koli.(Kande Gao)