Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 10:46:18    
Jaridar People's daily ta bayar da bayanin edita cewa ya kamata jama'ar kasar Sin su yi murmushi ga kasashen duniya

cri

Yau 30 ga wata, a albarkacin lokacin ranar da ta rage kwanaki 100 cif da za a bude gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing. Jaridar People's daily ta bayar da bayanin edita, inda ta jaddada cewa, ya kamata jama'ar kasar Sin su yi amfani da zarafin gasar wasannin Olympic ta Beijing don yin murmushi ga kasashen duniya.


A cikin bayyanin, an bayyana cewa, ko da yake wasu mutane masu kulla makirci sun yi yunkurin kawo cikas ga gasar wasannin Olympic ta Beijing da kuma shafe mata bakin fenti, amma ko kadan wannan ba zai canja aniyar da mutanen duniya da ta yi don nuna kauna ga gasar wasannin Olympic ba, haka kuma ko kusa ba zai sauya aniyar da mutanen Sin suka yi ta shirya gasar wasannin Olympic tare da nasara domin dukkan duniya ba.


Bayanin ya nuna cewa, aikin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya riga ya shiga lokacin karshe, kuma ana gudanar da dukkan ayyukan share fagen kamar yadda ya kamata, gwamnatin kasar Sin da jama'arta cike suke da imani da kwarewarsu wajen shirya wata gasar wasannin Olympic ta musamman bisa babban matsayin koli.(Bako)