Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-30 08:41:23    
Alkalan wasa na gasar wasannin Olympic ta zamanin da

cri

Alkalan wasa na gasar wasannin Olympic ta zamanin da suna da iko mai tsanani, wadannan alkalan wasa su kan sa riga mai launin jar garura, kuma su kan sa hular da aka yi da itacen zaitun a kansu, ban da wannan kuma, suna dauke da bulala mai alamar iko, idan 'yan wasa sun saba wa ka'ida, to, alkalan wasa za su yi musu bulala.

Ana iya cewa, ikon alkalan wasa na gasar wasannin Olympic ta da ya fi na zamanin yanzu. Kafin a fara gasar wasannin Olympic, 'yan wasa su kan taru a wani wurin dake kusa da wurin da za a shirya gasar wasannin Olympic domin koyon ka'idojin gasa, a sa'i daya kuma, alkalan wasa sun yi bincike iri daban daban ga 'yan wasa bisa ka'idojin da aka tsara. A cikin wata guda kafin a fara gasar, alkalan wasa su ma sun zama malaman koyar da wasa.

Kazalika, kafin aka bude gasar, alkalan wasa sun hau kan doki tare da wutar yular da aka dauka daga tsaunin Olympia domin ba da umurnin daina yaki ga birane na kasar Greece, ta haka, 'yan wasa sun je gasa daga wurare daban daban.

A gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da, aiki daban na alkalan wasa shi ne yi rantsuwa a gaban wurin ibada na Zeus tare da 'yan wasa, kuma za su shirya gasa da kuma yanke hukuncin gasa. Matsayin alkalan wasa a gun gasar wasannin Olympic ta zamanin da ya kai sama sosai, kuma a cikin farkon shekaru 200 da aka fara gasar, alkalin wasa shi ne sarki kasa, kuma shi daya kadai. Ya zuwa shekarar 480 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, alkalan wasa sun karu daga daya zuwa tara, ya zuwa shekarar 384 kafin haihuwar Annabi Isa alaihissalam, sun karu zuwa goma.

To, yaya aka hakake alkalan wasa su yanke hukunci bisa adalci? Domin wannan, a kan dauki matakai a jere, daya daga cikinsu wanda ya fi muhimmanci shi ne yi rantsuwa a gaban wurin ibada na Zeus, kowa ya sani, Zeus shi ne sarkin gumaka, alkalan wasa suna jin tsaronsa, shi ya sa a kullum sun yanke hukunci bisa adalci. (Jamila Zhou)