Ran 29 ga wata da dare, an fara mika wutar wasannin Olympics na Beijing a birnin Ho Chi Minh wanda ya zama zango na karshe na ayyukan mika wutar yola a ketare.
Mutum ta farko da ta mika wutar ita ce Madam Nguyen Thi Thu Ha mataimakiyar shugaba ta birnin Ho Chi Minh kuma ta shugaba ta kwamitin kula da ayyukan muka wutar yola na birnin Ho Chi Minh.

Ma'aikatan kamfannonin kasar Sin, da dalibai da Sinawa mazauna kasashen waje darurruka sun taru a inda za a fara mika wutar, suna daga tutoci, suna ba da kwarin gwiwa ga wasannin Olympics na Beijing.
|