Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 20:44:39    
Kabilar Dong a kauyen Zhaoxing

cri

Isowar wakilan CRI a gundumar Liping

A ci gaba da ziyararmu a lardin Guizhou, a ranar Alhamis 24 ga wata Aprilu, mun tashi daga birnin Guiyang, babban birnin lardin Guizhou, muka nufi kauyen Zhaoxing, inda al'ummar wannan kauye kabilar Dong ne. Wannan kauye na Zhaoxing yana cikin gundumar Liping.

Yayin da muka isa wannan kauye an yi mana kyakkywar marhabin, inda aka shirya wani kwarkwaryar buki na maraba da tawagar gidan rediyon CRI. A yayin wannan bukin, al'ummar wannan kauye sun yi mana nunin al'adunsu masu ban sha'awa.

Babban abu mafi ban sha'awa daga cikin al'adun kabilar Dong shi ne karrama bako cikin sakin fuska. Su kan karbi bako yayin da 'yam mata suke sanye da tufafin gargajiya masu launuka iri iri sun yi ado da kayan ado na azurfa, sun kuma sanya duwatsun wuya, da lika furanni a kai, samarinsu kuma sun yi ado da tufafi masu launin baki da wando da kuma rawani a kai, suna rera wakoki masu dadin ji.

Giya na da mahimmanci sosai ga kabilar Dong, don haka yayin da ake tarbar bako, yam mata su kan yi ado, suna rera waka tare da baiwa bako giya a bakinsa a matsayin nuna kauna da karramawa.

Wannan kabila ta Dong ta yi fice wajen iya rera wakoki, musamam idan aka yi la'akari da yadda wakokin wannan kabila suka yi fice a duniya. Daga cikin wakokin da suka yi fice akwai wakar da ake kira Galao da Geyi.

Duk da kasancewar yankunan da kabilar Dong ke zama tsaunuka ne suka mamaye su, amma babbar sana'ar wannan kabila ita ce noma, sabo da haka sun fi zama yankunan dake bakin kogi . Tsarin noma a tsakanin wannan kabila ta Dong bai bunkasa yadda ya kamata ba, domin kuwa suna amfani da sa ko doki wajen yin huda a gonaki. Kuma ba ya ga sana'ar noman, su kan yi kiwon dabbobi, musamman shanu. Kabilar Dong su kan zauna cikin rukuni na iyali, inda a tsarin zaman rayuwarsu, uba, ko kuma babban namiji a gida shi ne ke shugabancin harkokin iyali.

Kabilar Dong suna da wata fasaha ta yin amfani da katako zalla wajen gina gidajensu. Su kan yi irin wannan gida da katako ba tare da yin amfani da kusa ko guda ba. Kuma abin mamaki shi ne suna gina bene mai hawa a kalla biyar ko sama da haka, amma duk da katako zalla.

Daga cikin yawan jama'ar kabilar Dong a kasar Sin, wanda ya kai kimamin miliyan biyu da dubu dari tara da sittin, sama da kashin hamsin na zama a lardin Guizhou. Tarihi ya yi nuni da cewa, kabilar Dong ta samo asalinta ne daga kabilar Baiyue. Kabilar Dong tana da harshenta, amma babu haruffa, don haka suna amfani da haruffa Sinanci, kuma akasarin al'ummar wannan kabila sun iya harshen Han, wato Sinanci. Lawal daga kauyen Zhaoxing kabilar Dong da ke gundumar Liping ta lardin Guizhou.

gadar maganin iska da ruwa da ke kauyen Zhaoxing na kabilar Dong

Lawal yana tare da 'yan matan kabilar Dong

Lawal yana yawo a kauyen Zhaoxing na kabilar Dong

wata hasumiya daban ta kauyen Zhaoxing na kabilar Dong

'Yan kabilar Dong suna marhabin baki da abinci iri iri

yan matan kabilar Dong suna rera wakokin kayan goge na Pipa

yan matan Kabilar Dong suna waka suna marhabin baki