Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 20:09:32    
Ziyara a kauyen Biasha na kabilar Miao

cri

\

An zabi Lawal da ya zama ango na kabilar Miao a cikin wani wasan da aka yi a ran 26 ga watan

A ci gaba da ziyarar aikin mu a lardin Guizhou, a wannan rana ta 26 ga watan Afrilu, mun kai ziyara a kauyen Biasha dake cikin gundumar Liping ta lardin Guizhou.

Kauyen Biasha, karamin kauye ne na kabilar Miao, kuma yana cikin kwari wanda ke zagaye da manyan tsaunuka, kuma koramun ruwa suna gudana a wadannan kwaruruwa. Sabo da haka babbar sana'arsu ita ce noma.

Kabilar Miao suna ma'amala sosai da kabilar Dong, sabo da haka shi ya sanya al'adunsu suka yi kama da na juna. Musamman a fannnin rera wakoki, da karrama baki. Kazalika kuma a fanning tufafin al'adun wadannan kabilu sun yi kama da na juna, domin kuwa suna sanya bakaken tufafi, haka nan kuma mazaje na kabilun biyu suna daura rawani.

Kabiar Miao suna bin addinin gargajiya, inda suke bautawa kusheyin kakannin kakannisu. Wato wata al'ada ta ban ga wannan kabila ita ce, a duk lokacin da aka haifi jariri, to ana dasa bishiya a daidai ranar da aka haifi jaririn. Wannan bishiya za ta rinka girma tare da wannan da ko diya da aka haifa, har zuwa lokacin da ya mutu. To a lokacin da wannan mutum ya mutu sai kuma a sare wannan bishiya, wato ita ma karshen rayuwarta ya zo ke nan. To amma kuma ana dasa wata bishiyar ta daban a kan kabarin wannan mutum. Kuma ba za'a sare ta ba har abada. Don haka zuri'ar wannan mamaci za su rinka kai ziraya suna yin bauta ga wannan itaciya tare da nema kariya daga duk wani bala'i daga wannan itaciya.

Don haka, ko wane mutun dan kabilar Miao dake wannan kauye na Biasha yana da itaciya, wadda aka dasa tun ranar da aka haife shi. Kuma ba za'a sare ta ba har tsawon rayuwarsa. Bisa al'adar wannan kabila ta Miao, duk wanda ya sare wata itaciyar da aka dasa a kan kabarin wani mamaci, to hukuncinsa kisa ne. Ko da yake a wannan zamani na yanzu ba a yin haka ba.

Mazaje na kabilar Miao suna da wata al'ada ta daban wato al'adar mallakar bindiga. Ko wane namiji dan kabilar Miao wajibi ne ya mallaki bindiga. Abin da ya nuna cewa wadannan mutane jarumai ne kuma mayaka. Kuma har ya zuwa wannan zamani da muke ciki, wannan kabila tana nan rike da wannan al'ada, ko da yake a wannan zamani ba' a yin amfani da wadannan bindigogi domin yaki, sai dai domin tabbabtar da ganin wannan al'ada ba ta gushe ba.

Kamar kabilar Dong, ita ma kabilar Miao tana da al'adarta ta musamman wajen yin bukin aure. 'Yam mata su kan yi ado da tufafi masu launukan baki, kore da ja, yayin da samari suke sanya tufafi masu launin baki sannan kuma su daura rawani. A dandalin da ake gudanar da wannan shagali na bukin aure, a kan rera wakoki da raye raye ta yin amfani da kayan busa da aka yi da gorar bamboo. Yayin da ake wadannan bushe bushe da raye raye da wakoki, za'a ga wasu samari sun duko amarya a kan sanda zuwa dandalin bukin auren. Yayin da aka iso da amaryar, Ko wane saurayi ya kan yi kokarin kwace amaryar, amma dai daga bisani ango shi ne ke samun nasarar kwace amaryar.

A wannnan lokaci ne a wani dattijo zai zo a gaban ango da amarya dauke da wasu kananan kofunan giya da aka yi da gorar bamboo ya ajiye, sannan ya kunna turaren wuta, inda ango da amarya za su tsallaka, bayan sun tsallaka, sai kuma wata kawar amarya ta zo ta karbi kofin giya ta baiwa ango bakinsa, sannan a mikiwa wannan dattijo shi ma a kurbe, To daga nan an tabbatar da auren ango da amarya. Abu na karshe shi ne za'a kawo tire cike da kananan kulin shinkafa da aka kulla cikin ganyaye wanda ango zai rike, suna zagayawa tare da amarya tana rabawa baki, su kuma bakin suna zuba kudi a cikin tiren.

To sai dai wata al'ada daban dangane da aure a wannan kabila ta Miao shi ne, duk bayan an kammala wannan buki na aure, ango ba ya da iko tafiya da amaryarsa zuwa gidansa sai bayan shekaru ukku. Wata hikima da ta sanya ake yin haka shi ne domin auna irin hakurin ango. Wato na yin jira har tsawon shekaru ukku kafin a ba shi izinin daukar matarsa. (Lawal)

Lawal Mamuda yana kwace amariyarsa ta kabilar Miao

Lawal Mamuda yana rawa tare da 'yan matan kabilar Miao

Lawal ya zama ango na kabilar Miao a cikin wani wasa

Mutanen kabilar Miao suna aski da wuka

Wakiliyar Guizhou TV tana ganawa da Lawal Mamuda

Wata 'yar kabilar Dong tana saka

'Yan kabilar Miao suna kulle gashin kansu