Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 19:43:18    
Cibiyar tabbatar da tsaron kai ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta yi gaggarumin bikin rantsuwa

cri
Ran 29 ga wata, wato a jajibirin ranar da ya rage kwanaki 100 da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, a nan Beijing, cibiyar tabbatar da tsaron kai ta Beijing a gun gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta yi gaggarumin bikin rantsuwa a kwalejin horar da 'yan sanda na Beijing. Zhou Yongkang, mamban zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma sakataren hukumar siyasa da dokoki ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya halarci bikin, ya kuma ba da tutoci ga masu tabbatar da tsaron kai.

Kafin wannan gaggarumin bikin rantsuwa, bayan da ya saurari takaitaccen rahoto kan ayyukan tabbatar da tsaron kai a gun gasar wasannin Olympic ta Beijing, Mr. Zhou ya jaddada cewa, gudanar da ayyukan tabbatar da tsaron kai a gun gasar wasannin Olympic yadda ya kamata yana matsayin tushe ne wajen shirya gasar wasannin Olympic mai sigar musamman kuma mai matakin koli. Wajibi ne a gudanar da ayyukan tabbatar da tsaron kai yadda ya kamata domin samar da kyakkyawan muhalli wajen samun nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing.(Tasallah)