Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 19:27:38    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai kai wa Japan ziyara

cri
Ran 29 ga wata, a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, madam Jiang Yu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta sanar da cewa, shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai kai wa kasar Japan ziyarar aiki tun daga ran 6 zuwa ran 10 ga wata mai zuwa, bisa gayyatar da gwamnatin Japan ta yi masa.

Madam Jiang ta bayyana cewa, kyautatuwa da kuma bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da Japan sun dace da babbar moriyar jama'ar kasashen 2, haka kuma, sun ba da taimako wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a Asiya da yankin da suke ciki. Kasar Sin tana son gama kanta da Japan wajen ciyar da irin wannan dangantaka gaba, sa'an nan kuma, tana fatan ziyarar da shugaba Hu zai kai wa Japan za ta kara inganta amincewa da juna a tsakanin bangarorin 2 ta fuskar siyasa, da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, da habaka yin mu'amalar al'adun da ke dacewa da 'yan adam, kuma kasashen 2 za su yi kokari tare domin rika raya huldar da ke tsakaninsu domin moriyar juna daga manyan tsare-tsare.(Tasallah)