Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 17:23:23    
Gidan ibada na Wenmiao na birnin Zhengzhou a lardin Henan na kasar Sin

cri

Gidan ibada na Wenmiao, gidan ibada ne da Sinawa na zamanin da suka gina domin tunawa da Confucius, kwararre mai ilmin ba da ilmi na kasar Sin. Shi ne kuma wurin da masu koyo na kasar Sin suka taru a zamanin da. Yanzu bari in jagorance ku domin kai ziyara ga gidan ibada na Wenmiao da ke birnin Zhengzhou na lardin Henan da ke yankin tsakiya na kasar Sin, za ku ji dadin ziyararmu a wannan shahararren gidan ibada da ke kasancewar alama ce ta birnin Zhengzhou.

Birnin Zhengzhou, babban birnin lardin Henan, tsawon shekarunsa ya wuce dubu 8, yana daya daga cikin wuraren da al'ummar kasar Sin suka taba zama a can can can da. Gidan ibada na Wenmiao da ke cikin wannan tsohon birni yana da tarihi na tsawon shekaru dubu 1 da dari 9 ko fiye. A shekarar 2005, hukumar birnin Zhengzhou ta zuba kudin Sin yuan miliyan 30 ko fiye domin yi wa wannan gidan ibada kwaskwarima. Yanzu gidan ibada na Wen Miao da ke birnin Zhengzhou na da kyan gani sosai. (music)

Bayan da wani ya shiga gidan ibada na Wenmiao, sai da farko ya ga babban zauren Dachengdian, shi ne ginin gargajiya kawai da aka iya gani a cikin wannan gidan ibada na Wenmiao bayan da ya sha gamuwa da gobara sau da dama, kuma an sha yi masa kwaskwarima a cikin dubban shekaru da suka wuce. A gaban babban zauren, akwai wani icen ba da almond mai tsawon shekaru dari guda ko fiye, wanda ya kada rassansa a tsakanin rufin tsoffin gine-gine a gidan ibada na Wenmiao, ya kuma ga sauye-sauyen da wannan gidan ibada ya samu a idonsa.

A cikin babban zauren Dachengdian, wani rukunin kayayyakin gilas masu launuka daban daban wato coloured glaze a Turance na da daraja sosai. Masana masu ilmin gine-ginen gargajiya da yawa suna ganin cewa, wadannan kayayyaki na matsayin abun al'ajabi, ana adana su yadda ya kamata a cikin daruruwan shekaru da suka wuce, ba a fasa su ba. Su ne bangare mai daraja sosai na gidan ibada na Wenmiao da ke birnin Zhengzhou.

Baya da babban zauren Dachengdian, akwai wasu gine-ginen gargajiya da abin ya shafa. Yanzu a cikin wannan gidan ibada da aka yi tsit a wajen, an kebe dakunan da ke yammaci da gabashinsa zuwa dakunan karatu. Gidan ibada na Wenmiao da aka yi masa kwaskwarima ya sauke nauyin yada ilmin gargajiya na kasar Sin da nagartattun al'adun gargajiya na kasar Sin bisa wuyansa. Kamar yadda aka yi a da a kasar Sin, yara su kan zauna a kasa a wadannan dakunan karatu. Su kan karanta litattafan ilmin Confucius na gargajiya na kasar Sin.A cikin gidan ibada na Wenmiao, ana sake sauraren yara suna karanta litattafai bayan shekaru dari guda. Bin al'adar ba da ilmin gargajiya na kasar Sin ta fi nuna ma'ana mai zurfi ga gidan ibada na Wenmiao mai yawan tarihinsa na tsawon shekaru 1900 ko fiye.

Yanzu gidan ibada na Wenmiao yana tanadin tarihin birnin Zhengzhou da kuma al'adun gargajiya na wannan birni.