Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 16:10:58    
Mu fahimci ala'dun kasar Sin a kwalejin Confucius da ke kasar Afirka ta kudu

cri

A ran 25 ga wata a Jami'ar Stellenbosch ta kasar Afirka ta kudu, an shirya gasar share fage ta yankin kasar Afirka ta kudu ta gasar magana da Sinanci ta dalibai ta duniya ta karo ta 7. Wata yariniya mai suna Kettering Lithgow ta rera wata wakar gargajiya ta kasar Sin wato wakar furen jasmine, ta haka ne, ta nuna kwarewarta sosai wajen magana da Sinanci, sabo da haka ne ta zama ta farko a gun wannan gasa a yankin kasar Afirka ta kudu. Kettering Lithgow tana da wani sunan Sin wato Ma Jingxia.

'Dan karamin jakadan kasar Sin da ke birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu Mr. Shi Weiqiang ya bayyana a gun gasar share fage cewa, 'Kettering Lithgow tana da kwarewar magana da Sinanci sosai, har ina tsammanin wata basiniya take magana. Da nake jin wakar furen jasmine da take rera, ina tsammanin wata yarinya ta kudancin kasar Sin tana fadin labaran da ke cikin zuciyarta.'

Babban take na wannan gasar magana da Sinanci ta dalibai ta duniya ta karo ta 7 shi ne 'mu shiga cikin gasar wasannin Olympics mai himma, mu yi magana da Sinanci da farin ciki'. 'Yan takara su baki ne, kuma shekarunsu sun yi kasa da 30 da haihuwa, haka kuma su dalibai ne da ke karatu a jami'o'i. Abubuwan da ake yi cikin gasar sun hada da kwarewar magana da Sinanci, da ilmin kasar Sin, da al'adun kasar Sin da dai sauransu, domin bincike kan kwarewarsu ta magana da Sinanci a zaman yau da kullum.

'Dan karamin jakadan kasar Sin da ke birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu Mr. Shi Weiqiang ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa suka shirya gasar magana da Sinanci ta dalibai ta duniya a kusantowar lokacin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing a shekarar 2008 shi ne, domin samar da wani dandali ga matasa da ke koyon Sinanci da su gwada kwarewasu, da kuma kago wata damar koyi da juna da kuma yin mu'amala da juna, ta yadda za a iya ba da kwarin gwiwa gare su da su kara sha'awar koyon Sinanci, da kuma kara fahimtar Sinanci da al'adun kasar Sin.

Jami'ar Stellenbosch da ta kafu a shekarar 1866 ta zama daya daga cikin jami'o'i mafi kyau da tsawon tarihi a kasar Afirka ta kudu. A shekarar 2004, gwmanatocin Sin da Afirka ta kudu sun daddale wata yarjejeniyar kafa wata cibiyar nazarin kasar Sin, a lokacin kuma, sun tabbatar da cibiyar da ta zama wurin da aka kafa kwalejin Confucius.

Jami'ar Stellenbosch ta yanke shawarar mayar da kwalejin Confucius na jami'ar a matsayin wakiltar hukuma da ke yada al'adun kasar Sin a kasar Afirka ta kudu, har duk nahiyar Afirka. Bisa labarin da muka samu, an ce, daliban kwalejin Confucius na jami'ar Stellenbosch sun kafa wata kungiyar dalibai domin koyon Sinanci, a cikin lokaci ne, su kan shirya aikace aikace na al'adun kasar Sin cikin lokaci lokaci, da bikin nune nunen hotunan kasar Sin, da bikin abincin kasar Sin, da kuma bikin nune nunen fina finai na kasar Sin da dai sauransu. Tun daga shekarar 2005, kwalejin Confucius na jami'ar Stellenbosch ya kan tura nagartattun dalibai zuwa birnin Beijing, domin kara zurfafa ilminsu na Sinanci a ko wane zangon hutu na lokacin sanyi na ko wace shekara.(Danladi)