Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 16:02:57    
Kasar Sin na son yin kokari tare da kasar Japan don ciyar da dangantaka a tsakaninta da Japan gaba game da samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare

cri
A ran 29 ga wata a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, kasar Sin na son yin kokari tare da kasar Japan, don ciyar da dangantakar dake tsakaninta da Japan gaba ta yadda za su sami moriyar juna bisa manyan tsare-tsare.

Shugaba Hu Jintao ya gana da tsohon firayin ministan kasar Japan Mr. Nakasone Yasuhiro, inda ya ce, kasar Sin da kasar Japan dukkansu muhimmiyar kasa ce a nahiyar Asiya, haka kuma a duk duniya, raya dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Japan ta samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare wannan yana dacewa da babban moriyar kasashen biyu da jama'arsu, kuma yana da muhimmanci sosai ga zaman lafiya da bunkasuwa na Asiya, har ma na duk duniya. Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Japan, kuma tana tsayawa tsayin daka kan bin manufar zama tare cikin zaman lafiya, da sada zumanta daga zuri'a zuwa zuri'a, da samu moriyar juna, da kuma samu nbunkasuwa tare.

Ban da wannan kuma, shugaba Hu Jintao ya kara da cewa, kasar Sin ta nuna yabo da godiya ga gwamnatin kasar Japan sabo da tana tsayawa tsayin daka kan bin munufar kasar Sin daya tak a duniya kan batun Taiwan da na Tibet, da kuma nuna goyon baya ga kasar Sin da ta cimma nasarar shirya wasannin Olympic na Beijing.

Mr. Nakasone Yasuhiro kuma ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin Japan da Sin tana da muhimmanci sosai ga bunkasuwar kasashen biyu da na yankin gabashin Asiya. Ya kamata bangarorin biyu su nuna wa juna sahihanci, su nemi samun ra'ayoyi iri daya ba tare da yin la'akari da abubuwa da aka sha bamban a kansu ba, ya kamata su kafa dangantakar abokantaka cikin dogon lokaci bisa tushen yin tuba ga tarihi. (Zubairu)