Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 17:31:39    
wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

Jama'a masu sauraro, muna muku marahabin da sauraran shirinmu na "Kananan kabilun kasar Sin." Yanzu kuma za mu kawo muku ---- Bayan da aka murkushe munanan tashin-hankali da aka haddasa a ran 14 ga watan Maris a birnin Lhasa, an riga an fara yin bukukuwan addini yadda ya kamata a wuraren addini daban-daban na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta, jama'a masu bin addini na jahar Tibet sun samu tabbaci sosai wajen hakkin bin addini cikin 'yanci.

Mr. Ngpoi Jigyon, mataimakin sakataren kwamitin kula da harkokin addini na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, yanzu yawan manya da madaidaitan wuraren ibada na addinin Buddha na Tibet da ake da su a jihar ya kai fiye da 1,700, yawan 'yan budda maza da mata ya kai dubu 46.3. Bukukuwan addinai daban-daban suna gudana yadda ya kamata kuma sun samu girmamawa daga sassa daban-daban na zaman al'umma, ban da wannan kuma an kyautata wasu muhimman wuraren addini na jihar, kuma an ba da kariya ga muhimman littattafan addinin Budda da yawa na Tibet.

An bayyana cewa, gwamnatocin matakai daban-daban na jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta suna kulawa da zaman rayuwar sufaye, kuma sun shigar da su cikin tsarin samun tabbacin zaman al'umma. A farkon wannan shekara, mutane fiye da 50 da suka zo daga sassan addini sun ci zaben zama mambobin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na sabon zagaye na jihar Tibet.

---- Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ta tsaya kan bunkasa sana'o'i masu halayen musamman na faffadan tsauni ciki har da aikin noma da kiwon dabbobi da yawon shakatawa, ta yadda wadannan sana'o'i suka zama wani sabon tashe wajen bunkasa tattalin arzikin jihar.

An ce, cikin kusan shekaru 5 da suka wuce, jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta ware kudin Sin da yawansu ya kai fiye da Yuan biliyan daya domin tallafa da kuma bunkasa ayyuka kusan 200 masu halayen musamman wajen noma da kiwo , sabo da haka an kara samun ci gaba da sauri wajen gudanar da ayyukan noma da kiwo. Ban da wannan kuma bisa taimakon da gwamnati ta bayar, sana'ar yawon shakatawa tana ta zama wata sana'ar ginshiki ga tattalin arzikin jihar Tibet.

Ban da wannan kuma, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sana'ar yin magungunan jihar Tibet da sana'ar yin abinci masu inganci, da kuma sana'ar hannu na kabilar Tibet da sauran sana'o'i masu halayen musamman na jihar Tibet su ma suna ta samun bunkasuwa mai kyau.