Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 17:02:40    
Ana kyautata guraben zuba jari a birnin Dalian na kasar Sin don kara jawo kudin jari daga manyan kamfanonin kasa da kasa

cri

Birnin Dalian wani muhimmin birnin tattalin arziki ne da ke a arewa maso gabashin kasar Sin. Yanzu yana nan yana kara kyautata guraben zuba jari da bude wa kasashen waje kofa. Sa'an nan manyan kamfanonin kasa da kasa wadanda ke zuba jari a birnin kullum sai kara karuwa suke yi.

A kwanakin baya ba da dadewa ba, an kaddamar da babban kamfanin IMC mai jarin kasar Isra'ila kadai a yankin raya tattalin arzikin da fasaha na birnin Dalian. Kamfanin IMC yana sarrafa wukake masu inganci da ake amfani da su wajen yanyanka kayayyaki iri daban daban domin jiragen sama da motoci da kuma injuna da na'urori. Da Malam Du Hongwei, mataimakin babban majana na kamfanin ya tabo magana a kan yadda aka kafa kamfaninsa, sai ya ce, yayin da aka kafa kamfanin, an gamu da wata matsala, wato akwai wani bututun hayaki mai tsayin mita 30 kawai da ke daf da wurin da za a kafa kamfanin, mai yiwuwa ne, bututun zai kawo mugun tasiri ga muhallin kamfanin. Kamfanin ya damu da wannan sosai. Amma bayan da aka sanar da hukumar yankin raya tattalin arziki da fasaha na birnin Dalian, an kara daga tsayin bututun nan ba tare da wani jinkiri ba. Ta haka an daidaita wannan matsala. Malam Du ya kara da cewa, "kurar da wannan bututun hayaki mai tsayin mita 30 ke fitarwa za ta fada a kan wurin kamfanin. Sabo da haka hukumar yankin ya kashe kudi wajen daga tsayin bututun. Ta haka kurar ba ta iya faduwa a wurin kamfanin ba. Wannan ya gamsar da shugabannin kamfanin kwarai."

A shekarar nan, birnin Dalian ya kaddamar da wani kamfe na jawo jari daga kasashen waje don kafa masana'antu na zamani kuma ba tare da gurbata muhalli ba. Malam Mei Yuzheng, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin cinikin waje ta birnin Dalian ya bayyana cewa, makasudin gudanar da wannan kamfe shi ne, domin ba da kwarin gwiwa ga 'yan kasuwa na kasashen waje da su kara kafa masana'antu masu inganci da yawa a birnin Dalai, da samar musu da hidima da kyau. Ya ce, "shekarar nan shekara ce da muke jawo jari daga kasashen waje don kafa masana'antu masu inganci. Wannan ya dace da manufar gwamnatin kasar Sin game da samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya. Don haka yanzu muna neman jawo jari daga kasashen waje don kafa masana'antu na zamani wadanda ke iya samun riba mai yawa kuma ba tare da gurbata muhalli ba. "

A sakamakon matakan da birnin Dalian ya dauka wajen jawo jari daga kasashen waje da kyautata guraben zuba jari don samun ci gaba mai dorewa, an fara kafa masana'antu masu inganci da yawa a birnin wadanda suka hada da babban kamfanin IMC mai jarin kasar Isra'ila da ma'aikatar kera jiragen ruwa ta Dalian da babban kamfanin STX na kasar Korea ta Kudu ya zuba mata jarin dalar Amurka sama da miliyan 900 da kuma sauransu.

Haka kuma masana'antun da 'yan kasuwa na kasashen waje suka kafa bisa jarinsu a cikin shekaru da yawa da suka wuce, su ma suna ta kara bunkasa harkokinsu sannu a hankali. Da Mr Tokunori Nozawa, babban manaja na babban kamfanin yin kayayyakin gine-gine na Tostem na birnin Dalian ya tabo magana a kan wannan, sai ya ce, kamfaninmu ya sami babban taimako daga wajen manufofin nuna gatanci da birnin Dalian ya tsara. Nan gaba zai kara bunkasa harkokinsa. Ya kara da cewa, "bisa manufar nuna gatanci da birnin ya tsara, idan yawan kayayyakin da kamfaninmu ke sayarwa zuwa kasashen waje ya wuce kashi 70 cikin dari bisa duk kayayyakin da yake samarwa, to, yawan haraji da muke biya a kan kayayyakin zai ragu zuwa kashi 15 cikin dari. Ban da wannan kuma ta hanyar neman jawo jari daga kasashen waje, hukumar birnin Dalian ya sa kaimi da babban goyon baya ga kamfaninmu. " (Halilu)