Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 16:02:07    
An yi bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a birnin Pyongyang cikin nasara

cri

An yi bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a babban birnin kasar Koriya ta Arewa wato Pyongyang tare da cikakkiyar nasara yau 28 ga wata.

Birnin Pyongyang zango na 18 ne na bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing a kasashen ketare. Kazalika kuma, wannan shi ne karo na farko da wutar ta kai ga Pyongyang. An shafe awoyi 5 ana zagayawa da wutar, tsawon hanyar da aka bi ya kai kimanin kilomita 20. Gaba daya akwai masu rike da wutar gasar wasannin Olympics 80 wadanda suka halarci bikin, mai dauke da wutar na farko wani tsohon dan wasan kwallon kafa ne mai shekaru 72 da haihuwa mai suna Parg Doo Yig, mai dauke da wutar na karshe shi ne mataimakin sakatare-janar na kungiyar Marathon ta Koriya ta Arewa Zeng Seyg Ok. Jakadan Sin a Koriya ta Arewa Liu Xiaoming shi ma ya kasance cikin masu dauke da wutar gasar wasannin Olympics.

Bayan da aka yi bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing cikin nasara a birnin Pyongyang, za'a kai wutar a zango mai zuwa wato birnin Ho Chi Minh na kasar Vietnam.(Murtala)