Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-25 21:56:33    
shekaru 45 na sashen Hausa

cri

Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da war haka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a filinmu na "amsoshin wasikunku", kuma tun daga yau ne za mu fara gabatar muku da jerin shirye-shiryenmu na musamman da ke da taken "waiwaye adon tafiya", domin murnar cika shekaru 45 da sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki, kuma ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin.

Masu sauraro, kamar yadda kowa ya sani, a shekarun 1950 zuwa na 1960, kasashen Afirka da yawa na gwagwarmayyar neman 'yancin kansu, domin nuna goyon baya a gare su kuma, a karshen shekara ta 1960, gidan rediyon kasar Sin ya fara shirin kafa sashen Hausa. Amma a lokacin, Sinawa kusan ba wanda ya iya Hausa. Sabo da haka, a watan Janairu na shekara ta 1961, gidan rediyon kasar Sin ya gayyato wani masanin harshen Hausa mai suna Amada Bacha daga kasar Nijer, don ya koya wa wasu daliban kasar Sin wadanda suka iya Faransanci harshen Hausa, kuma malama Amina, tana daya daga cikinsu, ta ce, "Wannan masanin harshen Hausa ya kawo mana wani littafin Hausa, kuma sunan littafin (shi ne) 'ka yi karatu'. Kowace rana da safe, mun yi nazarin littafi tare da shi. Hanyarsa ta koyarwa kullum kamar haka, ya karanta kalma da kalma cikin Hausa, daga baya ya yi fassara da Faransanci."

Bisa kokarin da malamin da kuma dalibansa suka yi, wadannan dalibai sun fara iya Hausa sannu a hankali, kuma a ran 1 ga watan Yuni na shekara ta 1963, sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin ya fara aiki a hukunce. Ko kadan malama Amina ba za ta iya mantawa da wancan muhimmiyar rana har ba abada, ta ce, "Har abada, ba zan manta da wannan babbar rana ba. Domin tun daga safiyar ran 31 ga watan Mayu zuwa karfe 12 na dare a ran nan, mun yi aiki matuka, don gudun kuskure. Amada Bacha ya karanta labarai na minti kusan 15, bayan labarai, sai shirin fayafayai na minti 12 ko fi."

Masu sauraro, sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya fara aiki ne a ran 1 ga watan Yuni na shekarar 1963, wato yau da shekaru kusan 45 ke nan da kafuwar sashen Hausa na rediyon kasar Sin. Yanzu idan mun waiwayi wadannan shekaru 45 da suka wuce, za mu gane cewa, sashen Hausa ya bunkasa sosai, wato jariri ya girma ya zama dattijo ke nan.

Tun bayan da aka kafa sashen Hausa na rediyon kasar Sin, yau a kwana a tashi, sashen Hausa ya yi ta ci gaba a fannoni daban daban. Balarabe Shehu Ilelah, ma'aikacin sashen Hausa da ya zo daga kasar Nijeriya, wanda ya dade yana aiki a sashen Hausa, kuma ya gane ma idonsa bunkasuwar sashen Hausa, ya ce, "Da na zo sashen Hausa, a lokacin, sashen Hausa ba inda muke ba ne yanzu, a lokacin, yana wani babban titin da ake kira Fuxinmen, a wani ginin da ake kira Guangbo Dalou, tsohon gini ne, muna hade da ma'aikatar farfaganda ko watsa labarai, duk a wuri guda. A lokacin da muke sashen Hausa, muna amfani ne da irin tsohon faifan nan wanda ake nadewa, idan za mu yi labaru, sai a dauko, wani lokaci mu yanke, a murza da hannu. Sa'an nan, a lokacin, ofishinmu ba ya da kyau kamar yanzu, sabo da a lokacin, ofishinmu tsohon ofis ne, muna cunkushe da mutane, da yawa a ciki, har tebura ma ba su isa sosai ba, amma yanzu muna da yalwataccen ofis, kowa na da nasa bangare, kowa na zauna teburin zamani, wadda kusan bisa fahimtata, ba kowane gidan rediyo ne da ke watsa shirye-shiryen Hausa ke da irin sashenmu ba, na san gidajen rediyo da dama a duniya."

Ban da yanayin aiki, a farkon kafuwar sashen Hausa, ma'aikatansa 5 ne kawai, amma ga shi yanzu, Sinawa 13 tare kuma da takwarorinsu biyu da suka zo daga kasar Nijeriya suna aiki a sashen. Sa'an nan, shirye-shiryensu sun karu kuma sun kara inganta, har ma tsawon shirye-shiryen da yake gabatarwa a kowace rana ya karu daga rabin awa zuwa awa daya har zuwa awa shida.

Bunkasuwar sashen Hausa ba ya iya rabuwa da goyon bayan masu sauraronsa, kuma a cikin shekaru 45 da suka wuce, sashen Hausa ya samu karbuwa daga dimbin masu sauraronsa, ya kuma kulla zumunci sosai tare da su. Malam Salisu Muhammed Dawanau, mazaunin birnin Abuja, tarayyar Nijeriya, wanda ya fara sauraronmu tun daga shekarar 1987, ya ce, "A cikin shekarun da na saurari sashen Hausa, na fahimta sosai na kuma ilmantu, na tabbata sauran masu sauraronsu, wadanda suka fara saurare, ko dai kafin ni, ko bayan ni, su ma, ina da tabbacin, sun ilmantu, sun fahimci shirye-shiryensu, musamman sabo da fadin gaskiya da suke yi, da kuma shirye-shirye masu kayatarwa."

Halima, wata ma'aikaciyar sashen Hausa ba za ta iya mantawa da yadda masu sauraronmu suka karbe ta a lokacin da ta kai musu ziyara a jihar Bauchi a shekarar 1995. Ta ce, "wasu masu sauraronmu sun sami labarin zuwanmu a Bauchi, ba mu yi zaton cewar, wasu masu sauraronmu sun tare mu a kan hanyarmu zuwa wani wuri, sun gayyace mu zuwa shagunansu da gidajensu, da shigarmu a shagunansu ke da wuya, kai, abin mamaki da ya shiga idonmu shi ne, hotona da sauran hotunan ma'aikatan Sashen hausa suna jikin bangon shagunansu. Sun yi hira da mu cikin farin ciki sosai, sun dauki hotunanmu tare da su, sun ba mu shawarwari da yawa dangane da shirye-shiryenmu, har ma sun ba mu kyututtukan da suka shirya mana musamman."

Domin kara kawo wa masu sauraronsa labaran da ke faruwa a Afirka da dumi-duminsu, a shekarar 1995, sashen Hausa ya bude ofishinsa a birnin Ikko na kasar Nijeriya.

Bisa cigaban fasahar zamani, a shekarar 2003, sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya bude shafinsa na internet, wato hausa.cri.cn , a game da haka, Sanusi, shugaban sashen Hausa ya ce, "Makasudin kafa wannan shafin yanar gizo shi ne kara samar wa masu sauraronmu labarun duniya da suke bukata da sada zumunta a tsakaninmu da su. Shafin internet namu yana samun ci gaba cikin sauri. Yanzu, yawan masu karanta shafinmu na internet ya kai fiye da dubu 80 a kowane wata."

Jama'a masu sauraro, lokacin da sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin yake samun cigaba a fannin shafin yanar gizo, ya kuma samu ci gaba a fannin kafa gidan rediyo na FM a Afirka. A ran 10 ga watan Afrilu na shekarar 2006, sashen Hausa na CRI ya soma watsa shirye-shiryensa ta zangon FM na gidan R&M na birnin Yamai na Jumhuriyar Niger, inda yake watsa shirye-shiryenmu na awa 1 kowace rana a birnin Yamai, jamhuriyar Nijer. Daga baya kuma, a watan Oktoba na shekarar 2007, sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin ya soma watsa shirye-shiryensa har na tsawon sa'o'i 6 a kowace rana a birnin Yamai. A game da shirye-shiryen, Malam Mamane Ada, wani mai sauraronmu a birnin Yamai, wanda kuma ya kasance shugaban kungiyar Nesa ta zo kusa ta masu sauraronmu a birnin Yamai, ya bayyana mana cewa, shirye-shiryen sashen Hausa ya sami karbuwa sosai tun bayan da aka fara gabatar da su a birnin Yamai. Ya ce, "A ko yaushe, idan lokacin shirye-shiryen gidan rediyon Sin an fara shi, za a ga mutane kowa ya dauko rediyonsa, yana saurare."

Masu saurare, yau ga shi shekaru 45 sun wuce, har jariri ya girma ya zama dattijo. Kamar yadda Hausawa kan ce, "waiwaye adon tafiya", yau muna taya murnar cikon shekaru 45 da kafuwar sashen Hausa ne, ba ma kawai domin murnar nasarorin da muka cimma ba, amma domin murnar wannan sabon mafari a tarihin sashen Hausa, sabo da daga nan ne, sashen Hausa na rediyon kasar Sin zai fara sabuwar tafiya tare da samun sabon ci gaba.(Lubabatu)