Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-25 18:57:23    
Firaministan kasar Sin ya yi shawarwari tare da shugaban kwamitin EU

cri
Yau 25 ga wata a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya yi shawarwari tare da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Turai, Jose Manuel Durao Barroso, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyi sosai kuma cikin sahihanci a kan manyan batutuwan da ke shafar huldar da ke tsakanin Sin da Turai da kuma duniya baki daya, kuma suka cimma daidaito a kan batutuwa da dama.

Mr. Barroso ya iso birnin Beijing ne a jiya da yamma, don yin ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Sin. Yau da safe, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya yi shawarwari da shi. A cikin jawabin da ya yi wa kafofin yada labarai bayan taron, Mr.Barroso ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar da ke tsakanin Turai da Sin, ya ce,"Yau na zo tare da wakilai 9 na kwamitin kungiyar tarayyar Turai ne, da farko domin kara bunkasa huldar abokantaka da ke tsakaninmu da Sin. Hadin gwiwar da ke tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Sin zai iya kawo wa tarayyar Turai da Sin da kuma gamayyar kasa da kasa alheri. Lokacin da muke tunani kan kalubalen da ke gaban duniya baki daya, idan babu hadin kai tsakanin tarayyar Turai da Sin, to, ba za a iya samun wata kyakkyawar hanyar daidaita shi ba."

Firaminista Wen Jiabao da Mr.Barroso sun shafe kusan awa biyu da rabi suna shawarwari. Bayan shawarwarin, Mr.Wen Jiabao ya bayyana wa manema labarai na gida da na waje daidaiton da ya cimma tare da Mr.Barroso, ciki har da ci gaba da bunkasa huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Turai daga dukan fannoni da tabbatar da tuntubar juna a tsakanin manyan jami'ansu da kuma shawarwari a matakai daban daban da habaka hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki da dai sauransu. Mr.Wen Jiabao ya kuma bayyana wa manema labarai na gida da na waje makomar huldar da ke tsakanin Sin da Turai. Ya ce,"Inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Turai ya dace da moriyarsu, haka kuma ya dace da cigaban zamani. Moriya daya da ke tsakanin Sin da Turai ta wuce sabanin da ke tsakaninsu. Muddin mun girmama juna da amince da juna da yin koyi da juna da kuma hada gwiwa da juna, lallai, za a kara kyautata makomar huldar da ke tsakanin Sin da Turai."

Daga nasa bangaren kuma, Mr.Barroso ya ce, Turai na son kara karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninta da Sin, su hada kansu don fuskantar kalubalen da bunkasuwar duniya bai daya ta kawo. A lokacin da ya tabo magana a kan Tibet kuma, Mr.Barroso ya ce,"kungiyar tarayyar Turai na tsayawa kan bin manufar Sin daya tak a duniya da kuma girmama cikakkun yankunan kasar Sin da dinkuwarta, ciki har da Tibet. A ganin kungiyar tarayyar Turai, samun kwanciyar hankali da albarka a Sin na da muhimmanci kwarai da gaske ga gamayyar kasa da kasa. Ya kamata wasannin Olympics ya kasance kasaitaccen biki ga matasan duniya, kuma ya kamata a gudanar da shi yadda ya kamata, wannan kuma shi ne dalilin da ya sa na ki yarda da kauracewa wasannin Olympics. A ganina, ya kamata a gudanar da wasannin Olympics cikin ruwan sanyi."