Ran 24 ga watan Afril, tare da saukar wasu kungiyoyin yawon shakatawa na gida a birnin Lhasa bi da bi, ana farfado da kasuwar yawon shakatawa ta jihar Tibet da aka kawo cikas, a sakamakon da tashe-tashen hankulan da aka yi a birnin Lhasa a ran 14 ga watan Maris.
Wani jami'in hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ya bayyana cewa, tashe-tashen hankulan da aka yi a jihar Tibet a ran 14 ga watan Maris sun lalata sha'anin yawon shakatawa na jihar, daga bisani kuma sabili da tsaron kan fasinjoji, kamfanin yawon shakatwa daban daban na gida sun dakatar da karbar kungiyoyin yawon shakatawa da za su kai wa jihar Tibet ziyara.
Yanzu, ana farfado da zaman oda da doka na jihar Tibet kamar yadda ya kamata, kuma halin tsaron kai na zamantakewar al'umma ta jihar ya sami ci gaba, manyan kamfanin yawon shakatawa na jihar Tibet sun riga sun fara karbar kungiyoyin yawon shakatawa da suka zo daga sauran lardunan gida.(Bako)
|