Shugaban ofishin kula da harkokin fadar Budala ta birnin Lhasa na jihar Tibet mai suna Qamba Kelzang ya bayyana cewa, a tsohuwar jihar Tibet, fadar Budala ita ce ta Dalailama shi kadai kawai, yanzu, ita ce lu'u- lu'u mai daraja sosai na al'adun dukkan al'ummar kasar Sin. Ma'aikata 50 na ofishin kula da harkokin fadar da mabiyan addinin Budah fiye da 70 suna samar da hidima ga jama'a masu aikin ibada da masu yawon shakatawa na gida da na ketare da yawansu ya kai duban gomai a kowace shekara.
Qamba Kelzang mai shekaru 66 an haife shi ne a wani gida mai sukuni na iyalin Lhading na tsohuwar Tibet, kawunsa shi ne mai kula da harkokin gidan Dalailama na 14, kuma ya taba zama mai kula da harkokin gidan fadar Budala.
A shekarar 1989, an soma ayyukan yin kwskwarima kan fadar Budala, sai aka aiki Qamba Kelzang zuwa fadar Budala don kula da harkokin fadar, bayan shekaru biyu, an nada shi don ya zama shugaban ofishin kula da harkokin fadar.
Mr Qamba Kelzang ya yi alfahari da aikinsa. Ya bayyana cewa, a ganisa, tamkar yadda duk jama'ar duniya suke zura ido gare sa, duk saboda ba ma kawai wurin nan tsarkakken wuri ne na kabilar Tibet ba, hatta ma wurin nan wurin al'adun tarihi ne na duk duniya, yanzu ana nan ana yi mata kwaskwarima bisa babban mataki bayan shekaru 350 ko fiye.(Halima)
|