Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-25 14:11:16    
Kwamitin 'yan wasa na kwamitin wasannin Olympic na duniya ya bayar da sanarwa don yaki da nuna adawa ga gasar wasannin Olympic ta Beijing

cri

Kwamitin 'yan wasa na kwamitin wasannin Olympci na duniya ya bayar da sanarwa a ran 24 ga wata bisa agogon wuri a birnin Lausanne na kasar Switzerland cewa, ya nuna kiyayya ga adawa da gasar wasannin Olympic ta Beijing, yana ganin cewa, dole ne, a raba wasannin motsa jiki da siyasa.

Sanarwar da membobi 15 na kwamitin 'yan wasa na kwamitin wasannin Olympci na duniya suka bayar ta ce, nuna adawa da gasar wasannin Olympic ta Beijing ba shi da ma'ana ko kadan, amma zai kawo wa 'yan wasa cikas kawai, kuma bai dace da ra'ayin wasan motsa jiki na girmama da juna da sada zumanta da kuma zaman adalci ba.

Kazalika, sanarwar ta ce, ayyukan mika wutar yola sun alamantar da baza tunanin zaman lafiya a duk duniya, ya kamata a girmama wannan tunani, amma tarzomar da aka tada a lokacin mika wutar yola ta lalata wannan tunani.(Lami)