Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-25 13:23:08    
An soma nunin hotuna dangane da ziyara a biranen wasannin Olimpic a kasar Sin

cri
A ranar 24 ga watan Afril, a babban gini mai lamba 1 na filin jiragen sama na hedkwatar kasar Sin da ke birnin Beijing, an yi bikin nunin hotuna dangane da ziyara a biranen wasannin Olimpic na kasar Sin. Za a yi nunin a filayen jiragen sama na birnin Beijing da birnin Shanghai da sauran birane 5 da za su shirya wasannin Olimpic ko ba da taimako ga shirya wasannin Olimpic, za a nuna hotuna don bayyana shahararrun ni'imtattun wurare da zamantakewar al'umma da ke dacewa da 'yan adam da nasarorin da aka samu wajen ayyukan raya kasa da sauran abubuwa, sa'anan kuma an bayyana yadda jama'ar Sin suke sa ran alheri ga wasannin Olimpic da kuma halartar wasannin Olimpic da sadaukar da rai ga wasannin Olimpic.

Mun sami labari cewa, jakadan kasar Britaniya da ke kasar Sin Sir William Ehrman ya zo da kalmomin fatan alheri da firayim minista Gordon Brown ya rubuta domin nunin. A cikin wasikar sa ran alheri da shugaban kwamitin wasannin Olimpic na kasar Britaniya Mr Colin Moynihan ya bayyana cewa, tabban ne wasannin Olimpic na shekarar 2008 zai zama wata kasaitaccen bikin nuna murna dangane da duk 'yan adam da wasan motsa jiki wanda kuma ke dauke da halin wasannin Olimpic.(Halima)