Ran 24 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Sha Zukang mataimakin babban sakataren majalisar dinkin duniya ya nuna cewa, makarkashiyar bata wasannin Olympics na Beijing da 'yan neman 'yancin kan Tibet suka yi ba za ta sami nasara ba har abada.
A gun taron dandalin sauyawar yanayi da kirkira sabbin fasahohi da aka yi, Mr. Sha Zukang ya gana da manema labaru, inda ya ce, mummunan aikaci-aikacen da 'yan neman 'yancin kan Tibet suka yi sun goge idan jama'ar kasar Sin da jama'ar kasashen duniya, makarkashiyar bata wasannin Olympics na Beijing ba za ta sami nasara har abada ba.
Mr. Sha Zukang ya ce, "wasannin Olympics na Beijing shi ne wani babban batu na zaman al'ummomin kasar Sin da dukkan jama'ar kasashen duniya, na gaskata cewa, gwamnatin kasar Sin za ta yi wani wasannin Olympics mafi kyau tare da goyon bayan jama'ar kasar Sin."
|