Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-24 19:03:57    
Samun fahimta na dogaro da adalci

cri

Kwanan baya ba da dadewa ba, mamban kwamitin kungiyar tarayyar Turai a fannin cinikayya Mr.Peter Mandelson ya yi lacca a London, inda ya nuna rashin amincewarsa da yunkutin kaurace wa gasar wasannin Olympics ta Beijing domin a cewarsa hakan zai lahanta moriyar Turawa da kuma Sinawa. Mr. Mandelson ya kuma ce, a kan batun Tibet, kamata ya yi kasashen yammacin duniya su yi hadin gwiwa maimakon yin dagiya da kasar Sin.

In ba a manta ba, a matsayinsa na wani jami'in kungiyar tarayyar Turai mai kula da manufofin ciniki, Mr. Mandelson ya taba matsala lamba ba tare da tsangwama ba ga kasar Sin. Wassu kafofin yada labaru na kiransa ' Abokin karawa mai tsattsauran ra'ayi na kasar Sin a gun shawarwari'. Amma, laccar da Mr. Mandelson ya yi da kuma ra'ayoyin da wassu manyan jami'an siyasa, da masana da kwararru da kuma jama'a na kasashe da dama suka bayyana a kwanan baya don goyon bayan gasar wasannin Olympics ta Beijing da kuma nuna kiyayya ga yunkurin samun 'yancin kan Tibet. Wannan dai ya shaida cewa, har wa yau dai, yawancin jama'ar duniya suna duba kasar Sin bisa adalci da gaskiya duk da cewa wassu 'yan-a-ware na Tibet sun tada tarzoma ta hanyar yin amfani da gasar wasannin Olympics ta Beijing kuma wassu mutane dake da bakin nufi na yammacin duniya sun shafa wa kasar Sin bakin fanti ta yin amfani da wannan dama.

Mutane na kan cewa: samun fahimtar juna na dogaro da adalci. Dalilin da ya sa Mr. Mandelson ka iya duba kasar Sin bisa gaskiya shi ne domin sau tari neya taba yin cudanya tare da Sinawa. Saboda haka ne , ya sa shi ya fahimci kasar Sin sosai. Xing Ye, daraktan cibiyar nazarin harkokin kungiyar tarayyar Turai ta hukumar nazarin maganganun duniya ta kasar Sin ya furta cewa : ' Ga gaba daya, Mr. Mandelson ya tsayawa kan ra'ayin yin cudanya da kuma hadin gwiwa tare da kasar Sin. Ya yi haka ne domin ya ganam ma idonsa bunkasuwar kasar Sin, wadda take taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin kasashen duniya'.

Sa'anan Mr. Mandelson yana ganin cewa, moriyar kasashen Turai da kasar Sin a fannin tattalin arziki da cinikayya ba ta rabuwa; kuma manufar gyare-gyare da bude kofa da kuma samun ci gaba ta dace da moriyar kasashen Turai.

Aminai 'yan Afrika, ban da Mr. Mandelson, akwai sauran mutane masu tarin yawa na kasashen duniya da suka bayyana ra'ayin gaskiya kan batun Tibet saboda sun fahimci kasar Sin da kuma jihar Tibet ta kasar.

Mr. Thiru Na Ram, babban editan jaridar da ake kira ' Hindu' ya furta cewa : "Babu tantama, an samu ci gaba da saurin gaske a fannin hakkin bil adama a jihar Tibet, da lardin Sichuan, da lardin Gansu, da lardin Yunnan da kuma lardin Qinghai da dai sauran wuraren da 'yan kabilar Tibet. Lallai hakikanin yanayin bunkasuwar wadannan wurare ya sha bamban ainun da yadda Dalai Lama da kuma mabiyansa suka suka yi farfaganda a kai".

" Rashin sani, kukumi ne". Wassu kakofin yada labarai na yammacin duniya sun bayar da labarai marasa gaskiya a game da batun Tibet. A gun wani gangami da aka shirya a Paris, wassu dalibai Sinawa sun kirkira allunan nune-nune don bayyana wa Fransawa ainihin batun Tibet, inda wani dan kasar Fransa mai suna Pier ya fadi cewa : ' Lallai ba na amincewa da labaran da gidajen TV da kuma wassu kafofin watsa labaru suka bayar. Ina so in saurara da dubawa ni kaina'.

Gasar wasannin Olympics da za a gudanar a watan Agusta na wannan shekara a birnin Beijijg za ta samar wa mutane na kasashe daban-daban damar kara kusa da kasar Sin don fahimtarta. Wani Dalibi Basine dake Faransa ya bada goron gayyata ga Fransawa da su zo kasar Sin domin yin ziyara, ta yadda za su gano wata kasar Sin ta gaskiya. ( Sani Wang )