Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-24 17:52:41    
Bayani kan yadda Zhang Shuzhen ta yi noman ti

cri

Wakar da kuka ji waka ce da akan rera a yankin noman ti, a wane yanki na kasar Sin ake rera wannan waka a yanzu? Watakila kuna tsammani a yankin kudancin kasar Sin ne ake rera domin yana da dadadden tarihi wajen noman ti. A gaskiya dai ba gandun ti dake kudancin kasar Sin ne ake rera wannan waka, a wani sansanin noman ti na gundumar Shangnan ta lardin Shaaxi dake arewancin kasar Sin ne ake rera wannn waka mai dadi da kuka ji.

Kasar Sin tana da dadadden tarihi wajen noman ti, mutanen Sin suna masu ra'ayin cewa a kudancin kasar Sin kawai ana iya noman ti kawai. Duk da haka malama mai fasahar noman ti ta gundumar Shangnan ta samu nasarar noman ti a arewancin kasar Sin bayan da ta yi aikin tukuru tare da himma cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, ta dasa bishiyoyin ti a wuri mai tazara kilomita fiye da dari uku da yankin kudancin kasar Sin. Ta sa aya ga tarihi na sama da shekaru dubu biyu da ba a noma ti a arewancin kasar Sin, ta kuma taimakawa manoman da ke cikin yankin da take zama da su samu wadata.

Zhang Shuzhen, mata ce mai kiba kadan ba ta da tsawo, shekarunta sun kai saba'in. duk da haka ba ta jin gaji da aiki ba, ba ta so ta yi hutu ba. Ana iya ganinta a lambunan noman ti a yankin karkara na gundumar Shangnan. Manoma masu noman ti su kan kira ta "mama mai noman ti". Da wakilin gidan rediyonmu ya same ta, tana cikin gonar noman ti tana gyaran bishiyoyin ti.

Da aka yi magana kan noman ti a yankin gundumar Shangnan, sai a taba tarihin rayuwar Zhang Shuzhen. Dalili kuwa shi ne Zhang Shuzhen ta taka muhimmiyar rawa wajen noman ti a yankin gundumar Shangnan. Zhang Shuzhen ta kammala karatunta a jami'ar koyon ilimin dazuzzuka a shekara ta 1961. Da ta isa gundumar Shangnan, ta zama wata ma'aikaciyar gwamnati mai kula da dazuzzuka. A wancan lokaci, mutanen yankin gundumar Shangnan suna fama da talauci. Zhang Shuzhen ta ce kullum tana tunanin hada ilimin da ta koya daga jami'ar da aiki da zama na talakawa na yankin karkara, ta taba jarrabawar dasa wasu bishiyoyi masu daraja,amma ba ta samu nasara ba.

" Nauyin dake bisa wuyan ma'aikatan gwamnati masu kula da dazuzzuka, shi ne a canza yanayin zaman rayuwar mutanen da ke zama cikin duwatsu zuwa ga zaman rayuwar mawadata. Da farko na dasa bishiyoyi masu ba da mai, ban cimma burin da na zata ba. Yaya zan yi ko in sake shigo da bishiyoyi masu daraja daban in yi jarrabawa?"

Daga baya ta yi watsi da dabarar dasa bishiyoyi masu ba da mai, amma ba ta karaya ba, ta shiga nitsuwa ta fara nazarin ilimi dangane da tsire-tsiren dake cikin yankin Shangnan, tana fatan kubutar da talakawan da ke zama a wannan yanki daga talauci ta hanyar noman amfanin gona na sayarwa. Yankin Shangnan yana cikin duwatsun Qinglin inda yanayin sanyi da na zafi sun hadu, tsire-tsire sun yi yawan kwarai da gaske, da akwai wahaloli masu tarin yawa cikin tafiye tafiye a duwatsu. Zhang Shuzhen ta fidar tsoron wahala, ta sa kafa a kowane lungun yankin Shangnan. Ta gano cewa da ya ke yankin Shangnan yana cikin talauci, amma mutnen wurin sun fi kaunar shan ti. A ganinsu idan babu gishiri a cikin kwanaki ba kome, idan babu ti a rana daya su sha wahala. Shan ti ya zama dabi'u na mutanen wurin.

Yayin da take binciken dazuzzuka a kauyen Shuigou mai tazara sama da kilomita hamsin daga babban garin gunduma, Zhang Shuzhen ta yi sa'a ta gano bishiyoyin ti guda tara a wani karamin fili. Da ganin hakan tamkar ta sami wata nahiya sabo. Tana tsammanin tana iya dasa bishiyoyin ti a yankin Shangnan, ta iya noman ti a makeken fili na yankin Shangnan, mutanen wurin za su iya shan ti yadda suka ga dama, haka kuma za su iya samu karin kudin shiga ta hanyar noman ti. Daga nan Zhang Shuzhen ta fara da harkar noman ti.

Noman ti ba aiki mai sauki ba ne. Da ta fara noman ti, Zhang Shuzhen ta sha wahaloli da dama. Ta ce da ta fara noman ti, ta sha hassara. Daga baya ta gano cewa bishiyoyin ti sun fi bukatar yanayi mai kyau da kasa mai ni'ima. Aikin kula da bishiyoyin ti ba tamkar aikin kula da sauran amfanin gona ya ke ba. Ya kamata a sa lura sosai. A shekara ta 1970, Zhang Shuzhen ta samu ganyayen ti daga daga wani karamin filin bishiyoyin ti da take reno.

" A shekara ta 1970, na sami ganyayen ti kilo daya da digo tara kawai daga wani karamin lambun da na ke reno. Idan ina so in samu ganyayen ti masu yawa, sai a noma su a cikin yankunan da ke cikin duwatsu. Daga baya na dasa bishiyoyin ti a fili mai fadin kadada digo ashirin da shida, na sami nasara. "

Bayan da aka warware matsaloli dangane da shigo da bishiyoin ti massu nagari da kan yadda ake renonsu, sai matsalar kudi ta fito fili karara. A wancan lokaci, talakawa suna cikin talauci, ba zai yiwu ba da talakawan su bude lambunansu na bishiyoyin ti. Da ganin haka, Zhang Shuzhen ta nemi taimako daga gwamnati tana fatan bunkasa noman ti ta hanyar samun taimako daga gwamnatin gundumar Shangnan. A shekara ta 1972, ta yi rangadi a lambunan bishiyoyin ti na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin, ta ga yadda manoma suka samu wadata ta hanyar noman ti. Da ta koma gundumar Shangnan ta kawo shawarar noman ti ga shugabannin gundumar. Ta ce "Shugabannin gundumar Shangnan sun ba mu cikakken goyon baya wajen bude lambunan bishiyoyin ti masu tarin yawa. A shekara ta 1972, gwamnatin gundumar ta tura mutane sama da dubu ashirin zuwa duwatsun domin noman ti. Shugabannin gundumar sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa sha'anin noman ti a yankin gundumar.

Duk da haka gundumar Shangnan ta yi tafiyar hawainiya wajen bunkasa noman ti, tana bin tsarin bunkasa tattalin arziki bisa shiri. A farkon shekaru 1980, fadin filayen noman ti a gundumar Shangnan ya kai kimanin kadada miliyan hudu da dubu dari shida. Bayan da gwamnnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar kawo sauyi da bude kofa ga kasashen waje, Zhang Shuzhen ta ga zafafan burin manoma na kubutar da kansu daga kangin talauci da samu wadata. A wancan lokaci ana tafiyar da harkokin noman ti bisa gida da gida, da wuyan a baza fasahohi na zamani na noman ti tsakanin manoma masu noman ti, manoman ba su iya samun takamaman labarai na kasuwanni ba, su kan samu wahala wajen sayar da ganyayen ti. A shekara ta 1984, Zhang Shuzhen ta hada gandunan noman ti 37 a gundumar Shangnan ta kafa wani hadadden kamfanin mai kula da ti wanda ya hada ayyukan noman ti da gyara ti da kuma sayarwa, ta kuma zama mataimakiyar manaja ta kamfanin, a karo na farko ne ta kafa wata gada da ta hada "kasuwa da kamfani da sansani da kuma gidan manoma " wajen noman ti a gundumar Shangnan. Kamfanin ya ba da fasahohi ga manoma, yana bautawa manoma masu noman ti daga dukkan fannoni,ya kuma hada kasuwa da manoma masu noman ti, ya kuma ba da taimako ga manoma masu noman ti wajen warware matsalolin da suka fama da su.

A karkashin jagorancin kamfanin, fadin filayen noman ti ya wuce kadada miliyan 46 a shekara ta 2006, ganyayen ti da aka samu a shekara daya nauyinsu ya kai kilo rabin miliyan, darajarsu ta kai kudin Sin RMB yuan miliyan 23, noman ti ya kasance daya daga cikin manyan sana'o'i uku a gundumar Shangnan. Hadadden kamfanin ya kuma fitar da ganyayen ti iri iri na matsayin sama da na tsakiya da suka samu karbuwa a kasuwanni.

An daukaka Zhang Shunan a matsayin wanda ya kama gaba wajen yaki da talauci da ma'aikaciyar ba da misalin koyo wajen aiki na duk kasa sabo da babban taimakon da ya bayar wajen noman ti. Ta kuma sami mindar aiki na ran daya ga watan Mayu, mindar mafi daraja da gwamnatin kasar Sin ta baiwa ma'aikata. Duk da haka ba ta nuna girman kai ko kadan ba. Ta ce  "Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da jama'a suka tallafe ni, na kammala karatuna a jami'ar daga yarinya, kamata ya yi in mayar da martani ga zamantakewa. Wahaloli da talaucin da mutanen dake cikin duwatsun suka sha sun sa ni in yi kokarin samo dabarun wadatar da su, a ganina noman ti wata kyakkyawar sana'a ce da mutanen da ke zaune cikin duwatsu su sami wadata, ya kamata in nuna kwazo da himma waben yawaita ta. (Ali)