Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-24 17:48:43    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri

Asalam alaikum jama'a masu sauraro, barkanmu da wr haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan sabon shiri na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin wanda mu kan gabatar da shi a ko wane lahadi domin shere ku.Muna fatan za ku ji dadin shirin. Sai ku kutso akwatin rediyonku ku saurara.

An gano mitsitsin duwatsu 3956 a matsarmamar wani maras lafiya. An sami wani maras lafiya da ya karya matsayin kiwo lafiya a gundumar Dazhou ta lardin Sichuan na kasar Sin.Mutumin nan yana da shekaru 39 da haihuwa. bayan ya ji zafin ciwon ciki mai tsanani an yi masa fida.Ashe daga baya an gano mitsitsin duwasu 3,956 a cikin matsarmamarsa.Likitan da ya yi masa fida ya ce "lale wani matsayin koli ne da aka kago, ban taba ganin yawan kanana duwatsun da aka gano a cikin mutum daya.Likitan ya ce hakan ya same shi ne saboda maras lafiya ya bi wata hanyar cin abinci maras kyau.

Amintaccen amini. An sami wani tsohon nakasashe dake yawan shekaru 65 da haihuwa a gundumar Zigong na lardin Sichuan na kasar Sin yana da wani amintaccen amini wato kare ke nan da ake kiransa Fentiao.Karen Fentiao ya kan ja wani keke mai kafafuwa uku da wannan nakasashe ya zauna bisa daga wani wuri zuwa wani wurin daban. Wani aminin nakasashe ne ya ba shi wannan kare a watan Fabrairu na shekarar da ta shige. Karen ya fahimci duk wani umurnin da maigida ya bayar masa. Duk lokacin da maigida ya tafi waje, ya ja keken,har ma ya san lokacin da ya kamata ya tsaya yayin da ya ga alamun ja a gefen hanya.

Wani mai kanti ya yi gafara.A wata wasikar da ya aika wa wata jaridar wuri,wani mai kanti a birnin Duyun na lardin Guizhou ya nemi a yi masa gafara saboda ya kara fashin kaya a lokacin bikin yanayin bazara wato ranaikun bikin sabuwar shekara ta sinawa a duniya. mahukuntan kula da ciniki na birnin Duyun sun yi kashedi ga masu kantuna da masu mallakar motocin hawa kada su kar farashin kayayyaki da na hawa a ranaikun bikin sabuwar shekara, duk da haka wasu sun aikata laifi. Wani kakakin hukumar kula da ciniki ya ce mun riga mun yi wa wadanda suka yi kunnen uwar shegu da kashedi tara.

Wata mata tana son ta rage kibarta domin kasance siririya. Wata mata dake cikin birnin Nanchang na lardin Jiangxi tana fama da ciwon ciki, tana so ta samu magani a asibitin dab da gidanta a rakiyar mijinta. Abin mamaki ne ga mijinta da likita da suka gane matar ta samu ciwon ciki ne sabo da ta sa yatsar hannu ciki bakinta bayan ta ci abinci duk domin ta yi aman abincin da ta hadiye ta yadda ta kasance siririya. Ta yi hakan nan ne cikin watanni uku da suka shige har sau metan har zuwa ranar da ta sami magani a asibiti.

Tsofaffi suna fatan 'ya'yansu su kan kai musu ziyara. An sami wani tsoho a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake kudu maso gabacin kasar Sin wanda ya ke da 'ya'ya uku,dukkansu suna aiki a waje da birnin da tsoho ke zama a ciki. Duk da haka 'ya'yansa su kan kai masa ziyara a ranaikun bikin sabuwar shekara ta sinawa. Da wannan tsohon ya ga 'ya'yansa a bikin sabuwar shekara, amma ransa ya baci yayin da suka tashi daga gida zuwa wurarensu na aiki. Wani likitan da ya fi kwarewa a fannin kwakwalwa ya ce tsofaffi kamar wannan tsohon sun yi yawa suna jin kadaici a gidajensu sabo da 'ya'yansu suna nesa da gidajen,ya kuma yi fatan 'ya'yansu da su kan kai ziyara ga mahaifinsu a duk shekara.

Jama'a masu sauraro wannan ya kawo karshen shirinmu na labaru masu ban sha'awa na kasar Sin.Mun gode muku saboda kun saurarenmu ku huta lafiya.(Ali)