Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-24 17:42:57    
Kwas-kwasan sakandare na jihar Xinjiang da aka kafa a makarantun da ke birane masu cigaba

cri

A da, yin karatu a makarantun sakandare da ke birane masu cigaba, wannan ne wani mafarki mai nisa ga daliban sakandare da ke zama a jihar Xijiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur da ke yammacin kasar Sin. Amma, tun daga shekarar 2000 da gwamnatin kasar Sin ta soma kafa kwasa kwasan sakandare na jihar Xinjiang a makarantun da ke birane masu cigaba, wato ke nan wannan mafarki ba zai yi nisa ba, an zabi nagartatun dalibai a fannonin karatu da halayya da yawa na jihar Xinjiang zuwa birane masu cigaba, don yin karatu na sakandare.

A cikin dogon lokaci, a karkashin tasirin da aka kawowa a fannonin tarihi, da kuma tattalin arziki, da dai sauransu, ana kasance da babban gibi a tsakanin jihar Xinjiang da yankuna masu cigaba wajen bunkasuwar sha'anin ba da ilmi. Domin kara saurin horar da kwararru na kabilu daban daban na jihar Xinjiang, a shekarar 2000, gwamnatin kasar Sin ta tsaida wani kuduri, wato kafa kwas-kwasan sakandare na jihar Xinjiang a makarantun da ke birane masu cigaba, ciki har da Beijing, da Shanghai, da Tianjin, da Hangzhou, da dai sauransu, ta yadda za a iya kara ingancin ba da ilmi ga daliban kananan kabilu da ke yankuna masu fama da talauci ta hanyar yin amfani da fifiko na yankuna masu cigaba a fannonin tattalin arziki, da ba da ilmi.

A shekarar 2004, bayan da ya ci jarrabawa, dalibi Xepghet daga kabilar Uygur ya shiga kwas-kwasan jihar Xinjiang a wata makarantar sakandare da ke karkashin shugabancin jami'ar horar da malamai ta birnin Hangzhou. Xepghet wani tauraro ne a makarantarsu, ba kawai yana da maki mai kyau wajen karatu ba, har ma ya kwarre ne a fannoni daban daban. Yanzu ya dare kujerar mataimakin shugaban kungiyar dalibai ta makarantar, kullum yana shirya da halarci aikace-aikacen kai ziyara a lokacin hutu. Bayan da ya zo birnin Hangzhou, ya samu dama da yawa don yin cudanya da daliban da ke wurin, a lokacin da ya ke kokari kan karatunsa, a waje daya kuma, yana mayar da hankali kan kara kwarewarsa a dukkan fannoni, ya ce, "Yanzu, ba kawai kamfannoni masu samar da aikin yi suna kula da yawan ilmin da ka samu ba, har ma suna kula da kwarewarka. Saboda haka, ina sa himma domin shiga wasu ayyukan da kungiyoyin makarantarmu suka shirya, ta yadda zan iya kara kwarewata."

Iyayen Xepghet sun yi alfarma sosai saboda 'dansu ya shiga kwasa-kwasan sakandare a makarantar da ke birane masu cigaba. Yanzu, shekaru biyu sun wuce, Xepghet bai bata wa iyayensa rai ba, mamarsa ta yi godiya sosai ga kwasa-kwasan jihar Xinjiang. Ta gaya wa wakilinmu cewa, "Yankuna masu cigaba sun fi nuna fifiko wajen kafa makarantu, da kwarewar malamai, da kuma sauran fannoni, bayan haka kuma, daliban na iya bude idanunsu."

Domin sanya daliban jihar Xinjiang ke iya samun ilmi kamar yadda ya kamata, dukkan birane masu cigaba da ke kafa kwasa-kwasan sakandare na jihar Xinjiang, sun zabi shahararrun makarantu, don kafa kwasa-kwasan. A waje daya kuma, makarantu daban daban sun aika da malamai masu kyau zuwa kwasa-kwasan jihar Xinjiang, ba kawai wadannan malamai suna da karfi sosai wajen ba da ilmi ba, har ma suna mayar da dalibai daga jihar Xinjiang kamar yaransu.

A gidan Xepghet, wakilinmu ya gamu da malamai biyu na makarantar sakandare da ke karkashin shugabancin jami'ar horar da malamai ta birnin Hangzhou, sun zo nan musamman ne don karbar daliban da ke yin hutu a gidajensu, don gudun zafi da su koma makaranta. Malama Zhang Qi, sakatariyar kungiyar lig-lig ta matasa ta, ta gabatar da cewa, "Mu kan oda musu tikitocin jiragen kasa kafin su koma jihar Xinjiang, kuma mun kintsa kayayyaki na dukkan dalibai, daga baya kuma sai malamanmu sun raka musu koma jihar Xinjiang."

Tun shekaru 7 da suka wuce da aka kafa kwasa-kwasan sakandare na jihar Xinjiang a birane masu cigaba, an samu sakamako mai kyau. Ya zuwa yanzu, yawan daliban da aka karba ya kai sama da dubu 18, kuma daliban da suka gama karatu fiye da 3400 sun halarci jarrabawar shiga jami'ai, wadanda kashi 90 cikin dari daga cikinsu sun samu damar yin karatu a jami'ai. Behtiyar yana daya daga cikinsu.

A shekarar 2007, bayan da ya ci jarrabawa, sai Behtiyar ya soma karatunsa a sashen kimiyya na jami'ar Tianjin, babbansa yana jin farin ciki sosai, saboda Behtiyar ya shiga shahararriyar jami'a da ke yankuna masu cigaba, ya bayyana cewa, ya yi godiya sosai ga manufofin da gwamnatin kasar Sin ta dauka don nuna goyon baya ga aikin ba da ilmi na zaman al'umma, ya ce, "Kasarmu ta kafa kwasa-kwasan sakandare na jihar Xinjiang a makarantun da ke yankuna masu cigaba, wannan na da amfani sosai kan kara matsayin Sinanci na daliban kananan kabilu, da kuma kara kwarewar dalibai a dukkan fannoni, kazalika ya sa kami ga bunkasuwar ba da ilmi ta jihar Xinjiang. Ban da wannan kuma, ya rage nauyin da ke bisa wuyan iyalai na wadancan daliban da suka shiga kwasa-kwasan sakandare na jihar Xinjiang a fannin tattalin arziki, lallai yana da ma'ana sosai ga wadannan iyalan manoma da makiyaya masu fama da talauci."

Dilxat, ya fito daga wani iyalin manoma mai fama da talauci, ya shiga jami'ar Jilin bayan da ya gama karatunsa a makarantar sakandare ta biyar ta birnin Tianjin a shekarar 2007. Ya gabatar da cewa, a lokacin da yake karatu a kwasa-kwasan sakandare na jihar Xinjiang, makarantarsu ya samar da abinci masu inganci sosai, kuma a bikin babbar salla, da na karamar salla, malamai su kan shirya dukkan daliban da ke ajinsu don su fita waje da kuma cin abinci tare.

Kan zaman rayuwarsa a jami'a kuma, Dixat ya yi imani cewa, "Yanzu kasarmu ta kafa manufofin nuna fifiko da yawa, bayan haka kuma, jami'armu ta gabatar mana guraban aikin yi, don mu samun kudi da kanmu. Saboda haka, ba na jin nauyi sosai da ke bisa wuyana."

Ayyukan kafa kwasa-kwasan sakandare na jihar Xinjiang a makarantun da ke birane masu cigaba, ya samu goyon baya daga ma'aikatar ba da ilmi ta kasar Sin, da ma'aikatar kudi ta kasar, da biranen da abin yashafa, da kuma gwamnatin jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta bayar da kudin Sin RMB miliyan 400 kan kwasa-kwasan sakandare na jihar Xinjiang. Tun bayan da aka kafa kwasa-kwasan jihar Xinjiang kuma, ya samu karbuwa sosai daga jama'ar kabilu daban daban na jihar Xinjiang.