Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-24 17:25:07    
An kawo karshen aikin yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Bejing a birnin Canberra

cri

Yau 24 ga wata da yamma bisa agogon wurin, jirgin sama na musamman da ke dauke da fitilar wasannin Olympics na Beijing, ya tashi daga birnin Canberra, babban birnin kasar Australia, zuwa birnin Nagano na kasar Japan, wato zango na 16 da aka yi yawo da fitilar wasannin Olympics a kasashen ketare.



Birnin Canberra, zango ne na 15 da aka yi yawo da fitilar a kasashen ketare. Tsawon lokacin bikin ya kai awa biyu da minti 45, tsawon hanyar kuma ya kai kusan kilomita 16. Masu yin yawo da fitilar da yawansu ya kai 80 sun halarci bikin.

Bayan da aka kawo karshen bikin yin yawo da fitilar wasannin Olympics a birnin Canberra, hanyar da aka bi ta riga ta ketare manyan yankuna guda biyar na duniya. A ranar 26 ga wata, za a yi yawo da fitilar a birnin Nagano na kasar Japan. (Bilkisu)