Yau ran 24 ga wata, an cimma nasarar mika wutar wasannin Olympic na Beijing a birnin Canberra, hedkwatar kasar Australia.
Birnin Canberra tasha ta 15 ce da aka mika wutar wasannin Olympic na Beijing a kasashen waje. An shafe awa biyu da kuma minti 45 ana mika wutar, tsawon hanyar mika wutar kuma ya kai kusan kilomita 16. An fara daga filin "Reconciliation Place", a karshe kuma an kai filin wasan kwaikwayo mai lambar 88. Mutane 80 sun shiga aikin mika wutar nan, mutumin karshe dake mika wutar shi ne shahararen dan wasan iyo na kasar Australia Mr. Ian Thorpe, wanda ya taba samu lambobin zinari guda biyar a wasannin Olympic.
Bayan aka kammala aikin mika wutar a birnin Canberra, wutar wasannin Olympic na Beijing ta riga ta kai nahiyoyi biyar a duniya. Tasha mai zuwa ita ce birnin Nagano na kasar Japan. (Zubairu)
|