Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-23 21:25:07    
Rangadin aiki a lardin Guizhou

cri

Da misalign karfe 8:50 na safiyar Larabar nan ne muka tashi daga filin saukar jiragen Sama na birnin Beijing, muka kuma isa birnin Guiyang, babban birnin lardin Guizhuo da misali karfe 11:45.

Shugaban ofishin gidan Rdaiyon CRI a birnin Guiyang, Mr Wang shi ne ya tarbe mu a filin jirgin sama na Guiyang, inda daga nan ne muka isa masauki, wato Guizhou Hotel. Jim kadan bayan mun cin abinci sai kuma muka wuce taron manema labaru a hotel din Nenghui. Wanda aka shirya tsakanin Radiyon CRI da lardin Guizhou, taron daya samu halartar kafafen yada labaru da dama. Wannan taron manema labaru yana matsayin kaddamar da ziyarar aiki da tawagar gidar rediyon CRI ke yi a lardin Guizhou

Shugaban gidan talbijin na lardin Guizhou, Mr Bai Fengqin, shi ne ya bude taron tare da gabatar da jawabi. Kazalika ita ma Mrs Chen Yiqin, shugabar hukumar farfaganda ta lardin Guizhou ta gabatar da bayani.

A cikin jawabin da mataimakin shugaban rediyon CRI ya gabatar a wajen taron manema labarun, ya yi nuni da cewa tun shekara ta 2005 gidan rediyon CRI da lardin Guizhou suka fara hada guiwa domin tallata lardin na Guizhuo ga duniya ta hanyar CRI. Sannan kuma a shekara ta 2006 da shekara ta 2007, gidan radiyon CRI tare da larding Guizhou sun hada guiwa sun shirya wasu bukukuwa dangane da tallafawa kananan yara masu fama da talauci.

Kafin a kammala wannan taron manema labaru sai da mataimakin gwamnan lardin Guizhou ya kaddamar da shafin internet kan shirin shiga lardin Guizhou tare da wakokizi da lardin Guizhou da gidan rediyon CRI suke yi cikin hadin guiwa a lardin na Guizhou mai yanayi iri iri. Lawal Mamuda ya aiko daga birnin Guiyang.