Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-23 20:10:13    
An yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a Indenesia cikin halin annashuwa

cri

An yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a zango na 14 na ketare wato birnin Jakarta, hedkwatar kasar Indonesia a maraicen jiya Talata, agogon wurin. Jiya da maraice misalin karfe biyu, agogon wurin, an gudanar da gagarumin bikin yawo da fitilar Olympics na Beijing cikin kida mai fara'a a birnin Jakarta, babban birnin kasar Indonesia. Shugabar kwamitin wasannin Olympics na Indoneaia Madam Rita Subowo ta karbi fitilar wasannin daga hannun mataimakin shugaban zartarwa na kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing, Jiang Xiaoyu; daga baya dai ta mika ta ga mai dauke da fitilar wasannin na farko wato shugaban lardin Jakarta Mr.Fauzi Bowo, wanda ya yi farin ciki matuka da fadin cewa: " Yau dai, na yi alfamar samun damar zama mutum na farko mai dauke da fitilar wasanni. Na lashi takobin kammala wannan aiki mai ban girma".

A duk inda aka zagaya da fitilar wasannin Olympics na Beijing, ana iya jin amon ganguna da kide-kide da mutane masu tarin yawa musamman ma Sinawa dake zaune a can suka kada. Mr. Unardhi daga wata kungiyar 'yan makarantar Xinhua ya fada wa wakilinmu cewa, mun yi farin ciki da ganin Indonesia ta zama wata kasar da ta samu damar yin yawo da fitilar wasannin Olympics; kuma muna fatan 'yan wasa na Indonesia za su samu akiba mai tsoka a gun gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, a wannan rana, akwai wata kungiyar dalibai dake dalibci a Indonesia ta zo nan birnin Jakarta daga can nesa ba kusa ba na kasar, musamman domin bada kwarin gwiwa ga masu dauke da fitilar wasannin. Budurwa mai suna Zhang Morang yana daya daga cikinsu. Tana mai cewa : ' Mun iso nan ne yau da asuba. Amma jiya da dare ne muka taso daga wurin da muke zama cikin jirgin kasa. Muna kaunar kasar mahaifa kuma muna aiki tukuru wajen karatu. Muna tunawa da garinmu. Da zuciya daya ne muke fatan gasar wasannin Olympics ta Beijing za ta sami cikakkiyar nasara. Lallai mun bayyana damuwarmu kan yiwuwar samun matsala a nan bayan da muka ji labarin cewa an kawo cikas ga yin yawo da fitilar wasannin Olympics a yankin Turai. ''

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, 'yan wasa da kuma wadanda suka yi ritaya, wadanda suka fi shahara a kasar ta Indonesia, kusan dukkaninsu suna cikin takardar sunayen masu dauke da fitilar.Mr. Adhyaksa Dault, ministan kula da harkokin samari da na wasannin matsa jiki na Indonesia, da Mr. Yero Wacik, ministan al'adu da yawon shakatawa na kasar da kuma shugabar kwamitin wasannin Olympics na kasar Madam Rita Subowo da dai sauran jami'an gwamnatin kasar sun kammala aikinsu lami-lafiya a matsayin masu dauke da fitilar wasannin. Mr. Dault ya yi farin ciki matuka da fadin cewa :" Na yi alfaharin samun damar zagaya da fitilar wasanni a karshe a matsayin ministan samari da wasannin motsa jiki. Abin da nake so in fada, shi ne muna marhabin da zuwan fitilar wasannin Olympics a kasarmu. Kuma ina fatan hasashen wasannin Olympics zai farfado da wasannin motsa jiki na Indonesia".

An kawo karshen zagayawar fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Jakarta a maraicen jiya Talata misalin karfe uku da minti hamsin tare da nasara. Za a ci gaba da yin irin wannan rangadi mai jituwa ne a birnin Canberra na kasar Australiya.

Lallai fitilar wasannin ta samar wa Indonesia hasashen zaman lafiya da na zumunci, daidai kamar yadda Madam Rita ta fada cikin harshen Sinanci a gun bikin karshe na murnar yin yawo da fitilar wasannin cewa : Zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Indonesia ya dade ! ( Sani Wang )