Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-23 20:07:57    
Za a ji zafi a wasu bangarorin jiki sakamakon yin amfani da wayar salula fiye da kima

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "ilmin zaman rayuwa". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A cikin shirinmu na yau, za mu yi muku wani bayani kan cewa, Za a ji zafi a wasu bangarorin jiki sakamakon yin amfani da wayar salula fiye da kima.

A kwanan nan, likitocin kasar Amurka sun nuna cewa, yawan mutanen da suka jin zafi a wuyansu da babban yatsansu sakamakon yin amfani da wayar salula da MP3 da dai sauran kayayyakin lantarki cikin dogon lokaci ya samu karuwa cikin sauri, shi ya sa kamata ya yi a magance yin amfani da su cikin dogon lokaci da kuma kirkiro kyakkyawar dabi'a.

Stephen Conway, kakakin kungiyar yin jiyya ta hanyar motsa jiki ta kasar Amurka ya bayyana cewa, lokacin da ake kallon karamar fuskar wayar salula cikin dogon lokaci ko aikawa da gajerun sakwanni ba ji ba gani, a kan mai da hankali sosai a kan kamarar fuskar wayar salula, kuma a kan ajiye wayar salula a kasa, sabo da haka wannan zai haddasa rikewar jijiyoyi. Kuma kwararru suna ganin cewa, sabo da ana ta kara dogara da kayayyakin lantarki, shi ya sa irin wannan zafin da a kan ji zai zama ruwan dare.

Kuma Mr. Conway ya yi gargadin cewa, matasa sun fi saukin samun warkewa daga wannan zafin da suka ji sakamakon yin amfani da wayar salula, amma wannan zai sha bamban ga mutanen da shekarunsu ya yi yawa da haihuwa. Shi ya sa ya ba da shawarar cewa, lokacin da ake yin amfani da wayar salula da sauran kayayyakin lantarki da suke da fuska, ya kamata a kiyaye tsayinsu daga kasa ya yi daidai da na idanun mutane, kuma tsawon lokacin da ake dauka ka da ya zarce mintoci 10 ba.

Bisa wani sabon nazarin da manazarta na kasashen Sweden da Amurka suka yi, an ce, idan an yin amfani da wayar salula kafin a yi barci, to zai dauki tsawon lokaci kafin shiga halin barci mai nauyi, kuma za a rage lokacin barci mai nauyi.

Bisa kafofin watsa labarai na kasar Birtaniya suka bayar a kwanan nan, an ce, manazarta na kwalejin ilmin likitanci na Karolinska na kasar Sweden da jami'ar Uppsala ta kasar da kuma jami'ar Wayne ta jihar Michigan ta kasar Amurka sun gudanar da wani bincike ga maza 35 da mata 36 da shekarunsu ya kai 18 zuwa 45 da haihuwa. Wasu daga cikinsu suna da zama a cikin muhallin da ke da iska mai guba wanda ya yi daidai da na wayar salula, saura kuwa suna da zama a cikin muhalli maras iska mai guba.

Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, mutanen da suke da zama a cikin muhallin da ke da iska mai guba sun fi bukatar yawan lokuta wajen shiga halin barci mai nauyi, kuma yawan lokacin barci mai nauyi ya samu raguwa. Manazarta suna ganin cewa, mai yiyuwa ne iska mai guba da aka samu daga wayar salula tana iya sa kaimi ga tsarin mayar da martani kan abubuwan da suka faru ba zato ba tsammani da ke cikin kwakwalwa, ta haka mutane za su kara tada hankulansu, kuma za a raunana karfinsu na barci.

Ban da wannan kuma manazarta sun bayyana cewa, wannan bincike ya shaida cewa, labuddah iska mai guba da wayar salula ke fitarwa za ta yi illa ga kwakwalwa, shi ya sa ya kamata mutane musamman ma matasa su mai da hankali sosai a kan wannan sakamakon binciken. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da dimbin matasa sun saba da yin hira da abokansu ta wayar salula kafin su yi barci, wannan zai yi illa ga ingancin barcinsu sosai.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ce ke shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a