Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-23 10:23:05    
(Sabunta)Wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta isa birnin Canberra watau hedkwatar kasar Australia

cri

Ran 23 ga wata, da misali karfe 7 da minti 50 da safe agogon wurin, jirgin sama na musamman da ke dauke da wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing ya tashi daga Djakarta babban birnin kasar Indonesia zuwa birnin Canberra watau hedkwatar kasar Australia. Canberra ita ce tasha ta 15 ta mika wutar wasannin Olympic na Beijing, a sa'i daya kuma, ita ce tasha daya kawai da za a yi bikin mika wuta a nahiyar Oceania.

Babban direkta mai ba da umurni ga gudanar da bikin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing kuma mataimakin shugaba mai zartaswa na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Jiang Xiaoyu ya ba da takaitaccen bayyani a gun bikin maraba da wutar yola cewa, ya yi farin ciki da wutar yola ta wasannin Olympic na Beijing ta isa birnin Canberra, kasar Australia ta taba shirya wasannin Olympic na Beijing sau biyu, mun yi imani cewa, kasar Australia za ta kara fahimtar akidar Olympic ta "zaman lafiya da sada zumunta da samun ci gaba" da wutar yola ta kunshe.

Bisa shirin da aka yi, an ce, za a yi bikin mika wutar yola a birnin Canberra a ran 24 ga wata, da misali karfe 8 da rabi agogon wurin, masu mika fitila 80 za su fara mika wuta yola daga dandanlin sulhuntawar kasar da ke gabar tabkin Burley Griffin, kuma a kan hanyar, za su zarce babban dakin tunawa da yake-yake da kotun kolin kasar da laburaren kasar, da babban ginin majalisar dokokin kasar, a karshe dai za su iso wurin da suka sa niyya watau wurin shakatawa na tarayyar Australia, tsawon hanyar da za a bi wajen mika wutar yola zai kai kilomita 15, kuma za a kashe awo'i 3 wajen wannan bikin.(Bako)