" Kara ingantawa da kuma bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Fransa na dacewa da babbar moriyar kasashen biyu da kuma jama'arsu", kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta bayyana a yau Talata a nan Beijing, inda ta kuma furta cewa,bangaren kasar Sin yana fatan bangarorin biyu wato Sin da Fransa za su yi kokari tare don daukaka ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu lami-lafiya kuma cikin dogon lokaci duk bisa hangen nesa da kuma muhimman tsare-tsare.
Sa'annan Madam Jiang Yu ta fadi cewa, bisa gayyatar da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kuma hukumar nazarin harkokin waje ta kasar suke yi musu ne, shugaban majalisar dattawa ta Fransa Mr. Christian Poncelet da kuma tsohon firaministan kasar Mr. Jean-Raffarin suka kawo ziyara kasar Sin daya bayan baya a kwanan baya; Ban da wannan kuma, mashawarcin shugaban kasar Faransa a fannin harkokin waje shi ma zai kawo ziyara a kasar Sin daga ran 26 zuwa ran 27 ga watan dake tafe. Bangarorin biyu za su yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma sauran manyan maganganun da suka janyo hankulansu duka.
Kazalika, Madam Jiang Yu ta ce, wakilin musamman na kasar Sin Hu Jintao ya ziyarci kasar Faransa daga ran 18 zuwa 22 ga wata, inda ya mika wa shugaba Sarkozy wani sakon da shugaba Hu Jintao ya rubuta shi da kansa. A nasa bangaren, shugaba Sarkozy ya sake bayyana cewa, bangaren Faransa na mai da hankali sosai kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Faransa yayin da yake aiwatar da manufar kasar Sin daya tak a duniya kan batun Taiwan da na Tibet. Dadin dadawa, shugaba Sarkozy ya nuna fatan alheri ga gasar wasannin Olympics ta Beijing. ( Sani Wang )
|