Ran 21 ga wata, bisa gayyatar da gidan Rediyo Kasar Sin ya yi musu ne, maneman labarun kasar Rasha biyu wadanda suka taba neman labaru a jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin, sun shiga aikin wani shirin da Sashen Rashanci na Rediyo Kasar Sin ya shirya dangane da 'Tibet a idon manema labarun kasar Rasha'. Yayin da ake daukar murya, wadannan maneman labaru biyu sun amsa tambayoyn da masu karatu na tashar Internet ta Rediyo Kasar Sin suka gabatar cikin Rashanci da Sinanci, sun bayyana labarun da suka gani ko suka ji a jihar Tibet, kuma sun yi kira ga manema labaru na kasa da kasa da su tsaya kan matsayin adalci da gaskiya na bayar da labaru kan batun Tibet.
Bayan aukuwar tarzomar kai farmaki kan jama'a da farfasa kayayyaki da wawashe su da kuma sanya wa wurare wuta a birnin Lhasa na jihar Tibet a ran 14 ga watan jiya, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya taba dauki alkawari a tsanake cewa, za a gayyaci manema labaru na kasashen waje don su kai ziyara a jihar Tibet don neman labaru. Bayan haka, ba da dadewa ba, menama labaru sama da 10 na kasashen waje sun sami damar neman labaru a jihar Tibet. Malam Eugeny Soloviev, wakilin reshen kamfanin dillancin labaru na ITAR-TASS na kasar Rasha a birnin Beijing yana daya daga cikinsu. Ya bayyana cewa, "wannan kyakkyawar dama ce ga manema labaru. Za mu ganam ma idonmu da hasarar da aka sha daga wajen tarzomar da ta auku a birnin Lhasa."
Malam Eugeny Soloviev da sauran manema labaru na kasashen waje sun ganam ma dionsu da irin halin da ake ciki a birnin Lhasa na jihar Tibet. Ya kara da cewa, "mun ziyarci wata makarantar wadda 'yan tarzoma suka lalata ta a lokacin aukuwar tarzomar. Wannan ya bakanta rayukan mutane kwarai, sabo da tarzomar da aka shirya ta shafi yara. Wasu yara sun ji raunuka a cikiin tarzomar. A ganina, ko ta yaya ba a iya yafe wannan ba, daidai kamar yadda mu kan ce, yara sun fi kome gare mu! Bayan ziyarar wannan makaranta, mun yi bakin ciki kwarai."
To, yaya jama'a ke zaman rayuwarsu a yau a jihar Tibet? Ko daidai da labaru da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammaci suka bayar ko a'a, wato ko jama'a ke sha wahalar zama kuma ba su da 'yancin bin addini? Malam Andrei Kirillov, shugaban reshen kamfanin dillancin labaru na ITAR-TASS na kasar Rasha a birnin Beijing wanda ya taba shafe mako daya yana ziyarar neman labaru a jihar Tibet a yanayin zafi na shekarar bara, ya bayyana wa maneman albaru hotuna da yawa da ya dauka a wancan lokaci. Ya ce, "abubuwan da suka shaku cikin zuciyata, su ne jama'ar jihar Tibet suna jin dadin zamansu kwarai da gaske. Daga hotunan da na dauka a Tibet, na gano cewa, kusan dukkan mutanen da ke kan hotunan suna murmushi. Mun ziyarci wani gidan Ibadan da ke a cibiyar birnin Lhasa, daga hotunan da na dauka a wannan gidan Ibadan ma, na ga dukkan sufane samari ke murmushi. Abubuwan da na gani su ne, ana da 'yancin gudanar da harkokin addini yadda aka ga dama a jihar Tibet, ba a gamu da cikas ko kadan ba."
Amma yayin da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammaci ke bayar da labaru a kan tarzomar ran 14 ga watan jiya a jihar Tibet, sun jirkitar da gaskiyar labaru da gangan, sun zirgi gwamnatin kasar Sin don cim ma mummunan nufinsu, sun mayar da tarzomar da 'yan a-ware na Tibet suka shirya kamar wai 'zanga-zangar lumana', wannan ya gamu da kiyaya sosai daga wajen jama'ar kasar Sin. Malam Kirillov ya ce, wannan ya nuna ma'auna biyu da wasu kafofin watsa labaru na kasashen Yammaci suka dauka a kan wannan batu.
A karshen lokacin daukar murya, Malam Kirillov ya yi kira ga manema labaru na kasa da kasa da su bayar da labaru kan jihar Tibet cikin adalci da gaskiya. (Halilu)
|