
Yau 22 ga wata, an soma yin yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a birnin Djakarta, babban birnin kasar Indonesiya.
Birnin Djakarta zango ne na 14 da aka yi yawo da fitilar wasannin Olympics na Beijing a kasashen ketare. Tsawon lokacin aikin ya kai awoyi 2 da minti 30, masu yin yawo da fitilar da yawansu ya kai 80 sun halarci aikin.

Bayan da aka kawo karshen yin yawo da fitilar a birnin Gjakarta kuma, za a cigaba da aikin a zango na gaba, wato birnin Camberra, babban birnin kasar Australia. (Bilkisu)
|