Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 17:06:24    
Wasu kafofin watsa labaru na tekare sun bincika kansu game da labaran kasar Sin da kasashen yamma suka watsa ba bisa gaskiya ba

cri

A 'yan kwanakin baya, bi da bi ne, wasu kafofin watsa na ketare suka bayar da bayanai, inda suka bincika kansu game da labaran da kafofin watsa labaru suka bayar ba bisa gaskiya ba, a yayin da ake fara mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing.

A ran 21 ga wata, jaridar 'Le Figaro' ta kasar Faransa ta bayar da wani labari cewa, shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya rubuta wata wasikar nuna jejeto ga Madam Jin Jing mai daukar wutar yola, wadda aka kai mata farmaki a yayin da ake mika wutar yola a birnin Paris, haka kuma Mr. Sarkozy ya gayyaci Madam Jin Jing domin ta kai ziyara a kasar Faransa. An labarta cewa, a hakika dai, Mr. Sarkozy ya dauki wannan mataki ne domin kai suka ga danyen aiki da wasu 'yan Faransa suka yi a yayin da ake mika wutar yola.

Jaridar San Jose Mercury News ta kasar Amurka ta bayar da wani sharhi a ran 20 ga wata cewa cewa, an yi maraba sosai ga wutar yola ta gasar wasannin Olympics a kasashen Argentina, da Tanzania, da Oman, mika wutar yola a Asiya ta zama wani abun alfahari ga jama'ar wurin. Sharhin ya ci gaba da cewa, yana fatan jama'ar su maido da ra'ayoyin Oylmpics na wasanni, da gasanni, da abokantaka, domin fuskantar mika wutar yola da gasar wasannin Olympics za a shirya a nan gaban ba da dadewa ba.(Danladi)