Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 16:49:14    
Yancin bin addini a Tibet ta yau ya sha bambam da ta jiya

cri
A gun tattaunawa a karo na farko a kan hakkin dan Adam na Beijing da aka shirya a ran 21 ga wata a birnin Beijing, mataimakin shugaban jami'ar kabilu na kasar Sin Mr. Shesrab Nyima ya bayyana cewa, 'yancin bin addini a Tibet ta yau ya sha bambam da ta jiya.

Mr. Shesrab Nyima ya ce, a fili ne dokar wurin na tsohuwar Tibet ta tilasta wa jama'a a fannin bin addini. Tsohuwar dokar ba ta nuna girmamawa ga jama'ar Tibet ko kadan ba, haka kuma ta kare hakkin musamman, da matsayin maras daidaici tsakanin matane. Amma a cikin tsarin mulkin Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin, 'yancin bin addini wani muhimmin hakki ne na 'yan kasa.

Ban da wannan kuma, Mr. Shesrab Nyima ya ce, gwamnatin kasar Sin ta girmama 'yancin bin addini, ta girmama hakkin dan Adam, kuma an tanada su a cikin tsarin mulkin kasa da shari'a, sun shiga al'ada da al'adu na al'umma. (Zubairu)