Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 16:28:25    
Kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia

cri

A cikin shirinmu na yau, zan yi muku wani bayani kan kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia ta kasar Sin.

Kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin tana birnin Yinchuan, hedkwatar jihar, kuma an kafa ta a shekara ta 1985 domin horar da manya maza da mata masu aikin koyar da addinin Musulunci.

Shugaban kwalejin Su Yang ya gaya mini cewa, yanzu akwai malamai 51 da kuma dalibai 325 a cikin kwalejin, kuma muhimman darusan da ake koyarwa su ne harshen Larabci, da Alkur'ani, da labarin wali Muhamoud, da dokokin addinin Musulunci, da harshen Sinanci, da Turanci, da dai sauransu.

Yang Liangliang, wani dalibi ne a kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia. Ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ya zo kwalejin shi ne koyon al'adun Musulunci a maimakon harshen Larabci kawai. A shekara mai zuwa, zai gama karatu daga kwalejin, kuma yana cikin shirin zuwa jami'ar Musulunci ta kasa da kasa da ke kasar Pakistan don kara ilminsa. Kuma ya kara da cewa,

"bayan da na gama karatu daga jami'ar, zan komo gida na kuma zama wani malami, ba cikin kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci da kuma makarantun koyon harshen Larabci kawai ba. In an bukace ni, zan je ko wace jami'a don gudanar da aikin koyarwa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da bisa matsayina na wani musulmi na kasar Sin, kishin kasa ya zama wani abin da ke gaba da kome."

Kuma an bayyana cewa, ya zuwa yanzu dalibai kusan 1500 sun riga sun gama karatunsu daga kwalejin koyon ilmin addinin Musulunci ta jihar Ningxia, kuma suna gudanar da ayyukansu a fannoni daban daban da ke da nasaba da addinin Musulunci da kuma harshen Larabci. Ma Liqiang yana daya daga cikinsu, kuma yanzu shi ne shugaban ofishin kula da abincin musulmi na kwamitin kula da harkokin kabilu da addinai na birnin Yinchuan. Ya gaya mini cewa,

"bayan da muka gama karatu daga kwalejin, yawancinmu mun shiga gwamnatoci a matakai daban daban na kasar Sin don gudanar da ayyukan kabilu da addinai, kuma wasu abokan karatuna sun je kasashen waje kamar Libya da Saudi Arabia don kara ilminsu, haka kuma wasu daga cikinmu sun je biranen Guangzhou da Shenzhen da kuma Yiwu da ke kudancin kasar Sin don yin cinikayya tare da kasashen Larabawa."

Sabo da kwalejin tana koyar da ilmin addinin Musulunci, shi ya sa ta jawo hankulan kasashen Larabawa sosai. Lokacin da aka kafa ta, bankin raya kasashen musulunci na duniya ya samar da kudin taimako, haka kuma ya zuwa yanzu baki dubbai da suka zo daga kasashe fiye da 100 sun zo kwalejin don yin ziyara, ciki har da sarkin kasar Saudi Arabia da sarkin kasar Malaysia, da yariman daular hadaddun sarakunan Larabawa da dai sauransu. Sabo da haka, shugaba Su Yang na kwalejin ya bayyana cewa,

"kwalejin wata shaida ce wajen zumuncin da ke tsakanin Sin da kasashen Larabawa da ke shiyyar gabas ta tsakiya, haka kuma wata gada ce wajen hada Sin da kasashen Musulunci tare. Shi ya sa dole ne zai bayar da gudummowarsa wajen raya sha'anin addinin Musulunci a kasar Sin, da kara zumunci da cudanya tsakanin kasarmu da kasashe daban daban na Musulunci, da kuma sa kaimi ga aikin bude kofa ga kasashen waje da jihar Ningxia ke yi."(Kande Gao)