A cikin wasikar da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya aika wa mai mika wutar yula ta wasannin Olympic ta kasar Sin Jin Jing, ya sake yin Allah wadai da harin da aka kai wa wannan nakasassiyar 'yar wasa a birnin Paris.
Shugaban majalisar wakilan Faransa Christian Poncelet wanda ke yin ziyara a birnin Shanghai ya isar da wannan wasika zuwa ga Jin Jing a ran 21 ga wata.
Mr. Sarkozy ya nuna gaisuwa ga Jin Jing kuma ya ce, ya san lamarin da ya faru a hanyar mika wutar yula ya bata zukatan jama'ar kasar Sin. Musamman ma, ba wanda ke iya karbar harin da aka kai wa Jin Jing, ya la'anci wannan lamari sosai da sosai. Lamarin da tsirarrun mutane suka tada ba zai bayyana ra'ayin jama'ar Faransa ga jama'ar Sin.
Mr. Sarkozy ya kuma gayyaci Jin Jing da ta kai ziyara a Faransa.
Jin Jing ta bayyana cewa, abin da ta mika ba wutar wasannin Olympic kawai ba, hatta ma zumuncin da jama'ar Sin suke nuna wa jama'ar Faransa.(Lami)
|