Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 16:06:33    
Babu kasancewar babban yankin Tibet cikin tarihi, in ji kwararrun ilmin Tibet

cri

Jaridar People's Daily ta ran 22 ga wata ta bayar da labari game da masanin kimiyya na cibiyar nazari kan ilmin Tibet Lian Xiangmin, inda Mr. Lian ya furta cewa, babu kasancewar babban yankin Tibet cikin tarihi.

Wani muhimmin abu da Dalai Lama ya yi ikirari a kai game da hanyar daidaici shi ne, kafa babban yankin Tibet wanda ya hada da duk fadin tudun Qinghai da Tibet. Lian Xiangmin ya yi furuci game da wannan cewa, a cikin tarihi, babu kasancewar babban yankin Tibet. Wurare masu cin gashi kansu da aka samu a matsugunan kabilar Tibet daban daban sun samo asalinsu a cikin daddadden tarihi.

Mr. Lian Xiangmin ya ce, zance kan babban yankin Tibet ya fito a yayin da 'yan mulkin mallaka suka kai hari a kasar Sin a zamanin baya, shi wani mafarki na jawo baraka ga kasar Sin.

Mr. Lian Xiangmin ya kuma bayyana cewa, mutanen da yawa na kasashen duniya ba su san mazaunan tudun Qinghai da Tibet sun hada da kabilun Han da Mongolia da kuma Hui da dai sauran kananan kabilu, kungiyar Dalai Lama tana fatan za ta yaudari kofofin watsa labaru ta hanyar yin amfani da zancen babban yankin Tibet domin share fage ga aikin kawo baraka.

Kazalika, Mr. Lian Xiangmin ya nuna cewa, kafin shekarar 1959, gwamnatin jihar Tibet dake karkashin jagorancin Dalai Lama ba ta kula da harkokin yankuna a waje da jihar Tibet. Kungiyar Dalai Lama ta fahimta sosai cewa, ba za ta samu nasarar neman 'yancin kai ba, kuma ba za ta kafa babban yankin Tibet ba. Amma, danyen aikin da ta yi don yaudarar kafofin watsa labaru da kare kungiyar 'yan gudun hijira, kuma za ta yi amfani da su wajen neman farfado da ikon musamman na kungiyar bayi, da ikon kula da harkokin siyasa da addinai, wannan shi ne babbar moriyarta.(Lami)