Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 15:00:38    
An sami damar maido da shawarwarin Doha kuma mai yiyuwa ne kasashen Afirka za su sami moriya

cri

A ran 21 ga wata, an shiga kwanaki na biyu a gun taron kwamitin sa kaimi ga bunkasuwa da ciniki na duniya, wato kwamitin UNCTAD na karo na 12 da ake yi a Accra, babban birnin kasar Ghana, a gun "taron manyan jami'ai" da aka yi a wannan rana, an yi shawarwari kan yadda kasashen Afirka za su iya samun cigaba da kansu ta hanyar yin cinikin duniya. Kuma karuwar farashin hatsi na kasashen duniya zai sanya a maido da shawarwarin Doha, ko kasashen Afirka za su sami moriya? Sai ku saurari rahoton da wakilinmu Wei Xiangnan ya bayar daga gun taron.

Kamar Mr. Ban Ki-moon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya ce, an bude taron kwamitin UNCTAD na karo na 12 a yayin da ake samun matsaloli masu yawa kan tattalin arzikin duniya. A gun bikin bude taro da aka yi a ran 20, an taba yin shawarwari kan matsalar gaggawa ta karuwar farashin hatsi, ba a da wani zabi sai dai a yi shawarwari kan matsalar bunkasuwar kasashen Afirka wadda ta fi wuya. A dogon lokacin da ya gabata, kasashen Afirka suna cikin hali maras kyau a harkokin ciniyayyan duniya. Mr. Kagame shugaban kasar Ruwanda ya ce, "tsarin cinikin duniya ba ya dace da kasashen Afirka daga fannoni masu yawa, misalin rangwame da kasashe masu cigaban masana'autu ke zuba, da shinge mai tsawo na shiga cinikin duniya, da ikon mallakar ilmi. Dole ne kwamitin UNCTAD da kungiyar cinikayyan duniya, wato kungiyar WTO da sauran hukumomi su nuna goyon baya sosai ga kasashen Afirka domin warware wadannan matsaloli, ta haka za a iya tabbatar da kasashen Afirka za su iya shiga cinikin duniya cikin yanayi iri daya."

Mr. Kagame ya sami goyon baya daga sauran shguabnnin da ke halartar taron. Madam. Halonen shugabat kasar Finland ta ce, yayin da kasashe masu cigaban masana'antu ke ba da taimako ga kasashen Afirka, ya kamata su bude kofa ga kayayyakinsu. ta ce, "kasashe masu cigaba masana'antu suna taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga kasashen Afirka da su shiga hada hadar tattalin arzikin kasashen duniya. Ya kamata su ba da taimako ga kasashen Afirka, musamman ma kara shiga da kayayyaki daga Afirka. Muna bukatar kawar da shinge ga kayayyakin Afirka da su shiga kasuwanni, wannan zai kirkiro sharadi mai kyau ga kasashen Afirka da su shiga tatalin arzikin duniya."

Mr. Lamy babban direkatan kungiyar WTO ya ce, dole ne kasashen duniya su yi gyare-gyare kan tsarin cinikin duniya yayin da suke fuskantar matsalolin sauyawar yanayi, da karancin makamashi, da karuwar farashin hatsi. Ya ce, "Idan muna son tinkarar wadannan matsaloli ta hanyar ta fi kyau, dole ne muna bukatar gyara tsari, ya kamata wannan tsari ya fi dace da moriyar kasashe masu tasowa." Mr. Lamy ya nuna cewa, mai yiyuwa ne za a maido da shawarwarin Doha a cikin kwanaki masu zuwa, wannan zai ba da dama ga bunkasuwar kasashen Afirka. Ya ce, "idan a daddale yarjejeniya, yawan rangamen da kasashe masu cigaba masana'antu suke zuba a gida zai ragu kashi 75 cikin 100, kuma za su soke dukkan rangamen da suke zuba kan kayayyakin fici, kasashen Afirka za su sami moriya daga wannan."

A gun taron, Mr. Ban Ki-moon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya kalubalanci kasashe dabam daban da su kara yin kokari kan batun rangame na aikin noma da ke cikin shawarwarin Doha domin ba da taimaka ga kasashen Afirka da su sami damar bunkasuwa cikin cinikin duniya. Ya ce, "ya kamata a aiwatar da wani gagarumin canja a fannin aikin noma ta hanyar yin ciniki da zuba jari, ta haka domin kara karfin samar da kayayyakin noma a kasshen Afirka. Yanzu, karuwar farashin kayayyaki ta haifar da wani sharadi mafi kyau wajen kawar da rangamen da ake zubawa kan aikin noma da harajin kwastan da ake biya wadanda suka yi mummunan tasiri ga ciniki."

Yanzu, an riga an sami cigaba sosai kan aikin noma na shawarwarin Doha. Mr. Lamy ya fayyace cewa, mai yiyuwa ne za a daddale yarjejeniyar share fage a karshen watan Mayu. Kasashen Afirka za su sami tsarin ciniki mafi adalci, da yawan damar shiga kasuwannin kasashen duniya, kuma za su sami taimaka a jare, wannan zai sai kaimi ga bunkasuwar da aikin rage talauci da kansu.