
Ran 22 ga wata da sanyin safiya agogon wurin, jirgin sama na musamman mai dauke da wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing ya tashi daga Kuala lumpur babban birnin kasar Malaysia zuwa Djakarta watau hedkwatar kasar Indonesia.
Birnin Djakarta ita ce tasha ta 14 ta mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing. Za a mika wutar yola har awo'i 2 da rabi, a daukancin dai mutane 80 za su shiga ciki, mutumin da zai dauki wutar yola a karshe shi ne Taufik Hidayat wanda ya sami lambar zinariya a gun gasar wasannin badminton ta Olympic ta Anthen.

Bayan da aka kawo karshen mika wutar yola a birnin Djakarta, za a ci gaba da mika fitila a tashar Canberra watau hedkwatar kasar Australia.(Bako)
|