Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 12:42:24    
Shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Koriya ta arewa ya bayyana cewa za a mika wutar yola a Pyongyang cikin cikakkiyar nasara

cri
Ran 21 ga wata, a birnin Pyongyang, shugaban kwamitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic na kasar Koriya ta arewa kuma shugaban kwamiti mai ba da umurni ga wasannin motsa jiki na kasar, Mr Park Hak Seon ya bayyana cewa, tabbas ne za a iya mika wutar yola a birnin Pyongyang cikin cikakkiyar nasara.

A gun liyafar da aka shirya domin maraba da wutar gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan ranar a ofishin jakadancin Sin da ke kasar koriya ta arewa, Mr. Park Hak Seon ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic da za a yi a kasar Sin, ba ma kawai zai zama wani abin alfahari ne ga dukkan jama'ar Sin ba, har ma zai kasance wani abin farin ciki ga jama'ar kasar Koriya ta arewa. Bikin mika wuta da za a yi a birnin Pyongyang zai kara inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen koriya ta arewa da Sin, kuma za a kara sa kaimi ga mu'ammala da hadin gwiwa tsakanin sassan motsa jiki na kasashen nan biyu, kuma za a bayyana wa dukkan mutanen duniya dangantakar gargajiya da ke tsakanin koriya ta arewa da Sin.

Jakadan Sin da ke kasar Koriya ta arewa Liu Xiaoming ya bayyana cewa, bikin mika wuta da za a yi a Pyangyong ba ma kawai zai kara inganta dangantakar gargajiya tsakanin kasashen Sin da koriya ta arewa, har ma zai kara sa kaimi ga kasashen nan biyu da su yi mu'ammala da hadin gwiwa wajen motsa jiki da kuma al'adu.

Ran 28 ga wata, za a mika wutar yola a birnin Pyangyong. Wannan shi ne karo na farko da aka yi bikin mika fitila a Birnin.(Bako)