Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 12:37:32    
Yunkurin maida batun Tibet a matsayin batun duniya ba zai taimaka ba wajen cimma burin neman 'yancin kan Tibet

cri
Jaridar People's Daily da aka wallafa yau 22 ga wata ta bayar da wani bayani mai lakabi haka, duk wani yunkurin maida batun Tibet a matsayin batun duniya ba zai taimaka ba wajen cimma burin neman 'yancin kan Tibet.

Bayanin ya ce, a cikin 'yan kwanakin nan, yayin da 'yan tsirarrun mutanen kasashen yammacin duniya ke yunkurin rura wutar nuna adawa da kasar Sin, Dalai Lama shi ma yana zagayawa a ko'ina a duniya. Wasu mutane kalilan ne suke son matsawa kasar Sin lamba ta hanyar yin amfani da 'yan tsirarrun mutane mabiya Dalai, haka kuma wadannan mabiya Dalai suna son mayar da batun Tibet a matsayin wani batun duniya, ta haka za su matsa kaimi ga gwamnatin kasar Sin.

Bayanin ya kara da cewar, ya zuwa yanzu, babu wata kasa a duniya wadda ke amincewa da 'yancin kan Tibet. Ya kamata tsirarrun mutane mabiya Dalai Lama su kara sanin cewar, duk wani yunkurin da suke yi na maida batun Tibet a matsayin wani batun duniya zai ci tura! Batun Tibet batu ne wanda ke shafar ikon mallakar kasar Sin, shi ya sa ko da yake akwai wasu kasashe kalilan wadanda suke nuna goyon-baya, idan ana so a nemi 'yancin kan Tibet, to, jama'ar kasar Sin ba za su yarda ba, gamayyar kasa da kasa ma ba za su yarda ba! Tun daga barkewar munanan tashe-tashen hankula a yankin Tibet a ranar 14 ga watan Maris, Sinawa suna hada-kansu kwarai da gaske, haka kuma Sinawa 'yan kaka-gida a ketare suna zanga-zangar nuna adawa da duk wani yunkurin kawowa kasar Sin baraka. Wadannan al'amura sun shaida cewar, duk wani yunkurin maida batun Tibet a matsayin batun duniya ba zai taimaka ba wajen cimma burin neman 'yancin kan Tibet.(Murtala)