Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 10:35:03    
Kada a musunta nasarorin da kasar Sin ta samu kan kare hakkin dan Adam a Tiebt, in ji kwararrun hakkin bil'adama

cri
A wajen dandalin albarkacin baki kan hakkin bil'adama wanda aka shirya jiya 21 ga wata a nan birnin Beijing, kwararrun hakkin bil'adama na kasa da kasa sun bayyana cewar, a cikin 'yan shekarun nan, kada a musunta irin cigaban da aka samu wajen kiyaye hakkin dan Adam a kasar Sin, musamman ma a yankin Tibet.

Babban editan Jaridar The Hindu ta kasar Indiya Rahim-Han Lhamo ya kai ziyara har sau biyu zuwa Tibet a cikin jerin shekaru 7 da suka gabata. Ya ce, hakkin bil'adama ya samu bunkasuwa cikin sauri a matsugunan kabilar Tibet dake jihar Tibet, da lardunan Qinghai, da Yunnan da dai sauransu. Hakikanin halin da ake ciki a wadannan wurare ya sha banban kwata-kwata da irin abubuwan da Dalai Lama da tsirarrun 'yan a-ware masu neman 'yancin kan Tibet suke ikirari.

Ban da babban edita Rahim-Han Lhamo, bi da bi ne jami'ai da masana ilimi na kasashen waje da dama wadanda suka taba kai ziyara Tibet suka bayyana cewar, a ganinsu, Tibet wani yanki ne mai cikakken 'yancin kai wanda ke kara bude kofa ga kasashen ketare, kuma ta sami bunkasuwa kwarai da gaske. Kazalika kuma, mutanen Tibet suna jin dadin 'yancin kai da hakkin dan Adam iri daban-daban wadanda ba'a taba ganin irinsu ba a cikin tarihi, ciki har da hakkin bin addini cikin 'yanci, da ikon shiga harkokin siyasa.

A nata bangare kuma, wakiliyar koli kan hakkin bil'adama ta majalisar dokokin Ukraine Madam Nina Karpachova ta fadi cewar, akwai kabilu sama da 50 a kasar Sin, yanzu muna ganin cewa, kowace kabila na samun bunkasuwa da kyau. Kasar Sin tamkar abin koyi ne ga sauran kasashen duniya, ya kamata dukkanin kasashen duniya su koyi yadda kasar Sin take yi a fannin kiyaye hakkin dan Adam.(Murtala)