Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 09:25:49    
Ya kamata kasashen yammacin duniya su nuna goyon-baya ga gyare-gyaren Sin, a cewar kwararren Jamus

cri
Wani mashahurin kwararren kasar Jamus kan batun Sin, Thomas Heberer ya bayyana kwanan baya cewar, kamata ya yi kasashen yammacin duniya su goyi bayan Sin wajen yin kwaskwarima, kada su maida kasar Sin tamkar shaidaniya.

Mr. Heberer ya ce, akwai dalilai daban-daban wadanda suka haddasa a maida kasar Sin tamkar mummunar shaidaniya a kasar Jamus.Wadannan dalilai sun hada da, tun daga karshen shekaru 90 na karnin da ya gabata ne, kafofin yada labarai na Jamus suka kara bayar da munanan labarai dangane da halin da ake ciki a kasar Sin, haka kuma mutane da dama suka bayyana matukar nadamarsu kan yiwuwar kaurar masana'antun Jamus zuwa kasashen waje da matsalar kwaikwayar kayayyakin Jamus. Ya ce, abin da akasarin Jamusawa har ma dukkanin mutanen Turai suke sani game da kasar Sin da Tibet kalilan ne, shi ya sa sun fara imani da labaran da kafofin labarai na wurin suka ruwaito musu, amma kafofin yada labarai sukan maida hankulansu sosai kan batutuwan dake jawo hankulan mutane.

Mr. Heberer ya cigaba da cewar, kasar Sin na bunkasuwa kwarai da gaske bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofarta ga kasashen ketare. Sin na kara budewa kasashen waje kofa, haka kuma mutanenta na kara samun 'yanci. Akwai sauran rina a kaba dangane da aikin yin gyare-gyare a nan kasar Sin, wanda kuma ke bukatar dogon lokaci tare kuma da nuna cikakken hakuri, shi ya sa kamata ya yi kasar Jamus har ma da duk nahiyar Turai su dade da nuna goyon-baya gare ta.

Heberer ya cigaba da cewar, hanyar da ta fi dacewa da za'a bi wajen kawar da banbancin da manema labaru na wurin suke nunawa kasar Sin ita ce, fadada mu'amalar kai-tsaye tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasashen yammacin duniya, ta yadda jama'ar kasashen yamma za su kara fahimtar cigaban zamantakewar al'umma ta kasar Sin da tunanin jama'arta.(Murtala)